"Akwai Wata a Kasa": Sheikh Ahmad Gumi Ya Hango Manufar Sace Dalibai
- Sanannen malamin addinin Musulunci, Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya yi tsokaci kan karuwar sace-sacen dalibai a Najeriya
- Sheikh Ahmad Gumi ya nuna cewa akwai alaka tsakanin sace dalibai 'yan makaranta da zargin yi wa Kiristoci kisan kare dangi
- Malamin Musuluncin ya yi fatan cewa da yardar Allah matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a kasar nan ta kusa zuwa karshe
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Fitaccen malamin addinin Musulunci da ke Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya ya yi magana kan karuwar sace yara 'yan makaranta.
Sheikh Ahmad Gumi ya ce karuwar sace yaran 'yan makaranta da ke faruwa a 'yan kwanakin nan, an kitsa su ne domin tallafa wa abin da ya kira 'labarin karya na kisan kare dangi ga Kiristoci'.

Source: Facebook
Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana hakan ne a cikin martaninsa kan sace yara 'yan makaranta a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai
A ranar Litinin, 17 ga wata Nuwamban 2025, wasu 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci a wata makarantar sakandiren kwana a jihar Kebbi.
'Yan bindigan a yayin harin na makarantar GGCSS, Maga da ke karamar hukumar Danku/Wasagu sun yi awon gaba da dalibai mata zuwa cikin daji
Tsagerun sun kuma hallaka mataimakin shugaban makarantar wanda ya yi kokarin kare dalibai lokacin da suka kawo harin.
Hakazalika a ranar Juma'a, 21 ga watan Nuwamban 2025, wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da dalibai a jibar Neja.
'Yan bindigan wadana suka kao harin, sun sace daliban ne a makarantar makarantar St. Mary’s Catholic School da ke kauyen Papiri a karamar hukumar Agwara ta jihar Neja.
Sace daliban dai ya jawo suka daga cikin da wajen Najeriya, inda aka yi kira ga hukumomi da su yi gaggawar kubutar da su cikin aminci.
Me Sheikh Gumi ya ce kan sace dalibai?
Malamin addinin musuluncin ya bayyana cewa matsalar tsaro a Najeriya 'kamar kyandir ne mai ci gaba da konewa'.

Source: Facebook
Hakazalika, ya nuna cewa akwai abin da ake son a cimmawa kan sace daliban da 'yan bindiga ke yi.
“Karuwar sace yara 'yan makaranta a ’yan kwanakin nan an kulla shi ne domin tallafa wa labarin rashin kishin kasa na ‘kisan kare dangi ga Kiristoci’, kuma abin bakin ciki shi ne har yaran Musulmi ma ana sace su."
"Rashin tsaro a Najeriya tamkar kyandir ne mai ci da wuta, zai kare da ikon Allah."
- Sheikh Ahmad Abubakar Gumi
Majalisar dinkin duniya ta magantu kan sace dalibai
A wani labarin labarin kuma, kun ji cewa majalisar dinkin duniya, ta yi martani kan harin da 'yan bindiga suka kai a jihar Neja, inda suka sace wasu dalibai 'yan makaranta.
Majalisar dinkin duniya ta hannun mai magana da yawun bakinta, Stephane Dujarric, ta yi Allah wadai da sace daliban da 'yan bindigan suka yi.
Ta bukaci hukumomi da su dauki matakan da za su tabbatar da cewa an kubutar da daliban cikin gaggawa da koshin lafiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


