Ana Barazanar Dauke Wuta a Najeriya kan Lakadawa Ma'aikatan Lantarki Duka

Ana Barazanar Dauke Wuta a Najeriya kan Lakadawa Ma'aikatan Lantarki Duka

  • Ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta NUEE ta zargi ’yan sanda da kai farmaki ga wasu ma’aikatan ta a Imo
  • Saboda haka kungiyar ta umurci mambobinta su dakatar da tura wutar lantarki a Imo har sai an kare lafiyarsu gaba ɗaya
  • NUEE ta ce za ta tsananta matakin zuwa dakatar da wutar lantarki a fadin Najeriya idan ba a ɗauki mataki ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta Najeriya (NUEE) ta yi gargaɗin cewa za ta iya katse wutar lantarki a Najeriya.

Ta fadi haka tare da kafa sharadin cewa dole a magance abin da ta kira “tsagerancin jami’an ’yan sanda” a matattarar wutar Egbu 132/33kV da ke Imo.

Tushen Wutar lantarki
Wasu turakan wutar lantarki. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Vanguard ta wallafa cewa ƙungiyar ta yi magana ne bayan zargin hare-haren da aka kaiwa ma’aikatan TCN yayin da suke bakin aiki a Imo.

Kara karanta wannan

Kisan Kiristoci: CAN ta kira Trump kan taimakon Najeriya, yaki da ta'addanci

A cewar ƙungiyar, jami’an ’yan sanda da ake zargin suna aiki da umarnin gwamnatin jihar sun yi wa ma’aikatan TCN duka sannan sun tilasta musu aiki ƙarƙashin barazana.

Me ya jawo barazanar dauke wutar lantarki?

Kungiyar NUEE ta yi zargin cewa jami’an ’yan sanda sun afka cikin dakunan sarrafa wuta da karfi yayin da jami'anta ke aiki.

Ta ce an farfasa kayan aiki, an dakatar da ma'aikatan da karfin bindiga daga aiki, sannan aka tsare dukkan ma’aikatan da ke wurin.

A cewar bayanin, an buge ma’aikata, an yi musu barazana, hatta motoci, wayoyi da kwamfutocinsu sun lalace.

Ma'aikatan wutar lantarki
Wani ma'aikacin wutar lantarki a bakin aiki. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Ƙungiyar ta bayyana mamaki da takaici game da irin wannan mataki, tana mai cewa aikin da ’yan sanda suka yi ya sabawa dukkan ƙa’idojin tsaro da aiki.

Wannan ya sanya ƙungiyar NUEE ta umarci dukkan mambobinta da ke Imo su dakatar da aiki nan take.

Halin da ma'aikatan lantarki ke ciki

Kara karanta wannan

Abu ya kacame, sabon shugaban PDP da tsagin Wike na iya arangama a taro

NUEE ta ce ma’aikatan da aka yi wa duka suna bukatar kulawar likita, kuma ta buƙaci a saki mambobin da aka kama ba tare da wani sharadi ba.

Ƙungiyar ta dage cewa dole ne a maye gurbin kayan aikin da suka lalace yayin da aka far musu a bakin aiki.

Ta kuma bukaci gwamnatin tarayya, TCN da rundunar ’yan sanda su samar da cikakkiyar kariya ga ma’aikata kafin komawa bakin aiki.

Barazanar katse lantarki a fadin ƙasa

Ƙungiyar ta gargadi cewa idan ba a magance matsalolin da gaggawa ba, ba ta da zabi face dakatar da aiki a fadin kasa.

A cewar NUEE, ma'aikata ba za su cigaba da aiki a yanayin da ake musu barazana, duka da tsoratarwa ba.

Rahoton Channels TV ya ce sun ƙara jaddada cewa dakatar da aiki a Imo za ta cigaba har sai sun tabbatar da cewa babu wani haɗari ga ma’aikatan TCN.

Sai dai rundunar ’yan sandan jihar Imo ta yi watsi da zargin cewa jami’anta sun yi duka ko tsare ma’aikatan matattarar wutar.

Lantarki ta jawo tashin gobara a Kano

Kara karanta wannan

Duniya za ta kafa rundunar tsaro a Gaza, Falasdinawa za su iya samun 'yanci

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an hukumar kashe gobara a jihar Kano sun yi bayani kan wata wuta da ta tashi a kasuwa.

Hukumar kashe gobara ta ce matsalar wutar lantarki da ta tashi a kasuwar ne ta jawo lamarin a kasuwar Singa.

Duk da cewa wutar ba ta jawo asarar rayuka ba, rahotannin hukuma sun nuna cewa shaguna sama da 30 sun kone.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng