An Baza Sojoji a Abuja bayan Yunkurin Kashe A.M Yerima da Ya Yi Rikici da Wike
- Rahotanni sun ce an ga motocin dakarun sojoji takwas suna sintiri a Gado Nasko bayan zargin bin Lt. A.M. Yerima
- An ce mutane cikin manyan Hilux ba tare da lamba ba ne suka bishi daga NIPCO zuwa Gado Nasko da yamma
- Hakan na zuwa ne bayan rundunar ’yan sandan birnin tarayya Abuja ta fitar da rahoto game da zargin yunƙurin kisan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Rahotanni sun bayyana cewa rundunar sojoji ta tura jami’anta tare da motocin sintiri guda takwas zuwa yankin Gado Nasko domin ƙarin tsaro.
Wannan ya biyo bayan zargin cewa an bi jami’in sojan ruwan Najeriya, Lieutenant A.M. Yerima kwanaki bayan ya yi rikici da ministan Abuja.

Source: Facebook
Vanguard ta rahoto cewa ana hasashen an kara matakan tsaro a yankin ne domin kaucewa fitina da ake zargin za ta iya tashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An fara zargin ne bayan da wasu mutane cikin Hilux marasa lamba suka bi jami’in daga tashar NIPCO da ke kan titin Kubwa zuwa hanyar Gado Nasko.
Rahoton baza sojoji a yankin Abuja
Majiyoyin tsaro sun shaida cewa a misalin ƙarfe 7:00 na yamma, an ga jerin motocin sojoji guda takwas suna sintiri a titin Gado Nasko.
Rahotannin sun ce wannan mataki yana da nasaba da damuwar da ta taso bayan bin da ake zargin an yi wa Lt. A.M Yerima.
Wani soja ya bayyana cewa lamarin ya faru ne kusan ƙarfe 6:00 na yamma, kuma hakan ya haifar da daukar matakin gaggawa domin tabbatar da tsaron yankin da kuma kariyar jami’in.
Majiyoyin sun tabbatar da cewa ana bincike kan zargin bin jami’in, sai dai ba a fitar da cikakkun bayanai saboda tsare-tsaren bincike.
Martanin Rundunar ’yan Sandan Abuja
Rundunar ’yan sandan birnin tarayya ta musanta samun wani rahoto game da yunƙurin kisa ko bin jami’in. Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta bayyana cewa:
“Hankalin Rundunar ’yan sandan birnin tarayya ya kai kan wallafe-wallafen da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke zargin an yi yunƙurin kashe Lt. Ahmed Yerima.”
Punch ta rahoto ta cigaba da cewa:
“Rundunar na so ta fayyace cewa babu wani rahoto irin haka da aka kawo ko aka rubuta a ko’ina cikin babban birnin tarayya.
"Ana shawartar jama’a da su yi watsi da wannan bayanin na karya, su kuma daina yaɗa labaran da ba a tabbatar ba da za su iya tayar da hankalin jama’a.”

Source: Facebook
A cewarta, mahukunta suna buƙatar hadin kan jama’a:
“Ana shawartar mazauna yankin su ci gaba da zama cikin shiri tare da sanar da duk wani motsi da ake zargin yana da barazana ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.”
Umarnin Tinubu kan rikicin Wike da Yerima
A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta saka baki a rikicin da aka yi tsakanin Nyesom Wike da A.M Yerima a Abuja.
Bayanai sun nuna cewa umarnin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar ne ya sanya rikicin ya lafa sosai.

Kara karanta wannan
An fadi gaskiya kan ikirarin sace Birgediya Janar yayin gwabzawar sojoji da ISWAP
Haka zalika, majiyoyi sun bayyana cewa an janye manyan motocin da aka kai wajen da aka yi rikicin da nufin rusau.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

