A.M Yerima: Tsohon Jigon APC, Frank Ya Shawarci Tinubu Ya Ja Kunnen Wike

A.M Yerima: Tsohon Jigon APC, Frank Ya Shawarci Tinubu Ya Ja Kunnen Wike

  • Tsohon jagora a APC, Timi Frank ya bayyana takaici a kan rikicin Ministan Abuja, Nyesom Wike da jami'in sojan ruwa, A.M Yerima
  • Mista Timi Frank na ce takaddamar da ta shiga tsakanin Ministan da sojan ya nuna tsantsar zalamar mulki a gwamnatin Tinubu
  • Ya zargi Wike da daukar Abuja tamkar filayensa, tare da raina doka da umarnin kotu wajen yin gaban kansa a duk lokacin da ya ga dama

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –Timi Frank, tsohon mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC, ya yi kakkausar suka ga ministan birnin tarayya, Nyesom Wike kan sa-in-sa da A.M Yerima.

A ranar Talata ne aka rika yada wani faifan bidiyo, inda aka ga sojoji sun dakatar da Wike daga shiga wani filin ƙasa da ake cece-kuce a kai.

Kara karanta wannan

'Ka nemi kashe ni,' Wike ya yi martani mai zafi ga Buratai bayan rigima da soja

Timi Frank ya dura a kan Wike kan sa-in-sa da Yerma
Hoton Ministan Abuja, Nyesom Wike da A.M Yerima Hoto": Lere Olayinka
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa a cikin bidiyon, an ga Wike yana zazzafar musayar yawu da wani jami'in sojan ruwa, A.M Yerima a kan wani fili.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon jigon APC ya dura a kan Wike

Sahara reporters ta wallafa cewa a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Frank ya ce abin da ya faru ya nuna girman kai da wasu jami'an gwamnatin Bola Tinubu ke da shu.

Ya bayyana lamarin a matsayin alama ta lalacewar tsarin shugabanci a Najeriya da kuma barazana ga dimokuraɗiyya a kasar nan.

Mista Frank ya ce wannan rikici ba maganar fushi ko halin mutum ɗaya ba ce, amma yana nuni da tsananin lalacewar shugabanci a Najeriya.

Ya zargi Wike da daukar Abuja tamkar gadonsa, yana cewa salon mulkinsa mai tsauri da raina umarnin kotu sun tozarta aikin gwamnati.

Wike: Timi Frank ya shawarci Tinubu

Timi Frank ya kuma zargi Shugaba Bola Tinubu da yin shiru kan lamarin, yana mai cewa wannan shiru zai ƙarfafa rashin biyayya ga doka .

Kara karanta wannan

A.M Yerima da Wike: Jerin mutane 4 da ke da karfin ikon bai wa soja umarni a Najeriya

Timi Frank ya shawarci Tinubu ya ja kunnen Wike
Hoton Shugaban Najeriya, Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: UGC

Ya kara da cewa haka kuma ya zai nuna kamar akwai wadanda suka fi karfin doka, da za su yi abin da ransu ya so a gwamnatinsa.

A cewarsa, wannan rashin tsawatarwa daga shugaban ƙasa ya nuna fifita siyasa fiye da kyakkyawan shugabanci.

Frank ya yaba wa jami’in sojan ruwa da ya nuna ladabi da ƙwarewa, yana kiran abin da ya yi a matsayin kyakkyawan abin koyi na ƙwarewar soja da kishin ƙasa.

Ya ce a kowace al’umma mai mutunci, irin wannan hali ya cancanci yabo ko ma lambar yabo ta ƙasa.

Frank ya bukaci Tinubu ya ja kunnen Wike, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa tana mutunta doka, ladabi da kuma ƙoƙarin kare hukumomi.

Wike ya yi martani ga Buratai

A baya, mun wallafa cewa Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana takaicinsa kan yadda mutane ke fassara rikicin da ya shiga tsakaninsa da jami’in rundunar sojin ruwa a Abuja.

Kara karanta wannan

Matawalle ya ga laifin Wike a kan musayar yawu da A.M Yerima

A ranar Talata ce ce-ce-ku-ce ta barke a faɗin ƙasar bayan bidiyon yadda Wike ya yi cacar baki da A.M Yerima ya yadu a kafafen sada zumunta, inda jama'a ke ganin rashin kyautawar Wike.

A cikin martaninsa, Wike ya ce ba wanda ya isa ya koya masa ladabi ko yadda aikin gwamnati yake, musamman mutumin da ya zarga da yin katsalandan cikin harkar zaɓe lokacin 2019.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng