Sojoji da 'Yan Sanda Sun Ba Hammata Iska a Benue, an Ji Abin da Ya Faru

Sojoji da 'Yan Sanda Sun Ba Hammata Iska a Benue, an Ji Abin da Ya Faru

  • An samu sabani tsakanin dakarun sojojin Najeriya da wasu jami'an 'yan sanda a jihar Benue da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Sabanin da aka samu a tsakanin jami'an tsaron ya jawo an yi harbe-harbe wanda ya kai ga jikkata wani mutum
  • Lamarin dai ya auku ne bayan sojoji sun yi yunkurin tsayar da 'yan sanda a wani shingen binciken da suka sanya a kan hanya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Benue - Rikici ya barke tsakanin dakarun sojojin Najeriya da jami'an ‘yan sanda na rundunar Operation Zenda (JTF) a jihar Benue.

Rikicin wanda ya yi sanadiyyar raunata akalla mutum daya ya auku ne a garin Naka, hedkwatar karamar hukumar Gwer ta Yamma ta jihar Benue.

Sojoji sun yi arangama da 'yan sanda a Benue
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya da shugaban sojojin kasa Hoto: @PoliceNG, @NigeriaArmyInfo
Source: Twitter

Mazauna yankin sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta barke kan rashin tsaro a Katsina, an samu asarar rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji da 'yan sanda sun yi arangama

Rikicin ya jefa al’umma cikin tashin hankali a garin wanda yawancin mutanen da ke cikinsa ‘yan gudun hijira ne.

An kuma gano cewa motar ofishin kwamandan rundunar JTF, CSP Lyam Akegh, ta lalace sakamakon harbin bindiga yayin arangamar.

Wasu ganau sun ce jami’an JTF suna dawowa daga aikin sintiri da ya shafi yaki da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a kan titunan Makurdi–Naka–Adoka–Ankpa da Naka–Agagbe, lokacin da sojojin da ke shingen bincike a yankin suka tsayar da su.

“A lokacin ne aka samu jayayya tsakanin jami’an tsaron, kafin daga baya a fara jin harbe-harbe a iska, wanda ya sa mutane suka rika gudu don neman mafaka."

- Wani mazaunin yankin

A cewar mazauna yankin, har zuwa yammacin Laraba, akwai wasu yara da ba a gansu ba, yayin da har yanzu ba a tabbatar da ainihin dalilin arangamar ba.

Me ya haddasa rikicin?

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun tarwatsa yunkurin sace jami'ansu da limamin addini a Abuja

Sai dai wata majiyar tsaro da ta nemi a boye sunanta ta bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan sojoji a wani shingen bincike sun ga wasu babura da ke dauke da naman saniya da aka yanka, wanda hakan ya basu mamaki.

“Sojojin sun yi ƙoƙarin tsayar da su domin bincike, amma sai wata motar Hilux ta karaso cikin gudu ba tare da ta tsaya ba. Sojojin sun yi harbi na gargadi, amma motar ta wuce har cikin garin Naka."

- Wata majiya

Ta kara da cewa daga baya an ji harbe-harbe a garin, kuma an gano cewa wasu jami’an Operation Zenda ne suka yi harbi a iska cikin murna bayan sun kammala nasarar wani aiki.

Sojoji sun fafata da 'yan sanda a Benue
Taswirar jihar Benue, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Abin da hukumomi suka ce kan lamarin

Har yanzu rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS) ba ta fitar da sanarwa kan ainihin abin da ya haifar da rikicin ba.

Haka kuma, mai magana da yawun ‘yan sanda ta jihar Benue, DSP Udeme Edet, ta tabbatar da cewa ana gudanar da bincike don gano musabbabin rikicin.

Ta bayyana cewa an fara tattaunawa domin warware sabanin da ke tsakanin jami’an tsaron.

A nasa bangaren, mai ba da shawara na musamman ga gwamnan jihar Benue kan tsaro da harkokin cikin gida, Joseph Har, ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan lamarin ba.

Kara karanta wannan

Ko me ya yi zafi: Sojoji sun budewa 'yan sandan da ke dawowa daga zaben Anambra wuta

Sojoji sun ceto 'yan NYSC

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun ceto wasu matasa masu yi wa kasa hidima a jihar Borno.

Sojojin sun kubutar da matasan ne a hanyar Buratai–Kamuya, bayan motocinsu sun lalace a wajen da 'yan ta'adda ke kai komo.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa dakarun sojoji sun yi gaggawar raka matasan daga Maiduguri zuwa Damaturu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng