Gwamnatin Tinubu Ta Dakatar da Batun Karbar Harajin Shigo da Fetur na Kashi 15

Gwamnatin Tinubu Ta Dakatar da Batun Karbar Harajin Shigo da Fetur na Kashi 15

  • Hukumar NMDPRA ta ce an dakatar da aiwatar da harajin shigo da man fetur da dizal da aka tsara na kashi 15
  • NMDPRA ta tabbatar da cewa akwai wadataccen man fetur da dizal a kasar nan domin biyan bukatar jama’a
  • Ta gargadi dillalai da ’yan kasuwar mai da su guji boye mai ko kara farashi ba bisa ka’ida ba a fadin kasar nan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta dakatar da aiwatar da tsarin karɓar harajin shigo da mai da dizal na kashi 15 wanda aka tsara a baya.

Wannan na zuwa ne bayan fitar da sanarwa daga hukumar NMDPRA a ranar Alhamis, wacce ta bayyana cewa an janye aiwatar da shirin.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: UGC

Punch ta wallafa cewa daraktan sashen hulda da jama’a na hukumar, George Ene-Ita ne ya sanya hannu a kan sanarwar da aka fitar.

Kara karanta wannan

Bayan gargadin Birtaniya, gwamnatin Tinubu ta fitar da sakamakon yaki da ta'addanci na 2025

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A baya, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da shirin saka wannan haraji domin karfafa tattali, sai dai gwamnatin ta sauya matsaya bayan nazari kan tasirin hakan a kan farashin mai.

NMDPRA ta ce akwai mai a Najeriya

A cewar hukumar, Najeriya na da isasshen mai da dizal a yanzu domin biyan bukatar jama’a a dukkan bangarori na kasa, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar karin amfani da mai.

Sanarwar ta ce:

“Akwai wadatar man fetur, dizal da iskar gas a cikin gida wanda ake samu daga matatun cikin gida da kuma ta hanyar shigo da kaya daga waje, domin tabbatar da cewa dukkan wuraren ajiya da tashoshin sayar da mai suna da isasshen kaya.”

Hukumar ta kuma bayyana cewa tana ci gaba da lura da yanayin wadatar kayayyakin mai a fadin kasa, tare da daukar matakan da suka dace don hana tangarda ko tashin farashi marar dalili.

Kara karanta wannan

'Yan Amurka sun shiga tsaka mai wuya bayan sabanin Trump da majalisa

An gargadi masu boye mai a Najeriya

Hukumar NMDPRA ta yi kira ga ’yan kasuwa da masu rarraba mai da su guji boye kaya ko yin karin farashi ba bisa yanayin kasuwa ba.

Mutane a gidan mai
Masu babura suna shan fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Channes TV ya nuna cewa hukumar ta ce boye mai zai iya haifar da matsalolin karancin fetur a wasu yankuna.

Ta ce:

“NMDPRA na amfani da wannan dama wajen jan hankalin jama’a da masu kasuwanci da su guji boye kaya ko kuma kara farashin man fetur da dizal ba bisa ka’ida ba.”

NMDPRA ta jaddada cewa tana aiki kafada da kafada da duk masu ruwa da tsaki a bangaren makamashi domin tabbatar da cewa akwai wadataccen mai a duk fadin kasar.

Tinubu ya yi kira ga 'yan jaridan Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga 'yan jarida su rika masa adalci wajen sukar manufofinsa.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne yayin taron 'yan jarida karo na 21 da aka gudanar a birnin tarayya Abuja ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Amurka ta shiga matsalar jiragen sama yayin da Trump ke barazana ga Najeriya

Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta dauki wasu matakai masu tsauri domin habaka tattalin arziki kuma da sannu za a ci moriyarsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng