Tsohon Hafsun Tsaro, Janar Chiristopher Musa Ya Samu Sabon Mukami a Amurka
- Janar Christopher Gwabin Musa ya samu sabon mukami a cibiyar Midlothian Angel Network da ke kasar Amurka
- An nada Janar Musa ne kwanaki kadan bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke shi a hafsun tsaron kasa
- Hukumar ta bayyana cewa kwarewa da jagorancin Janar Musa sun dace da burinta na gina tsarin saka jari mai ɗorewa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, ya samu babban mukami a kasar waje bayan fita daga aikin soja a watan Oktoba, 2025.
An nada shi a matsayin ɗaya daga cikin mambobin majalisar gudanarwa ta Midlothian Angel Network (Midlo).

Source: Twitter
The Guardian ta wallafa cewa Midlo wata cibiyar saka jari ce da ke Amurka wadda ke ƙara bunƙasa dangantaka tsakanin masu saka jari daga Amurka da Afirka.

Kara karanta wannan
Barazanar Trump: Gwamnatin Tinubu ta fadi halin da ake ciki kan tattaunawa da Amurka
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta sanar da wannan a cikin wata takardar da ta fitar, inda ta ce wannan na cikin shirin ta na ƙara haɗa yankuna biyu wajen kirkire-kirkire da saka jari.
Janar Musa ya samu sabon mukami
Shugabar hukumar Midlo, Tomie Balogun, ta bayyana cewa nada Janar Musa wata alama ce ta ci gaba a burin hukumar na ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin Amurka da Afirka.
Tomie Balogun ta ce:
“Shigowar Janar Musa cikin majalisar gudanarwa wani babban mataki ne a kokarinmu na samar da shugabanci mai hangen nesa da kyakkyawar hulɗa tsakanin kasashen duniya.
"Jarumtaka, jajircewa da hangen nesa na jagoranci suna nuna ginshiƙan dabi’un da Midlo ke tsayawa akai.”
Ta kuma bayyana cewa hukumar ta dauki nauyin shirin karatunsa na Stanford GSB domin ci gaba da horar da shugabannin da ke tafiyar da harkokin saka jari.
Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya tabbatar da samun mukamin a wani sako da ya wallafa a X.
Karin bayani kan mukamin Janar Musa
A nasa bangaren, wani jami;in Midlo, Wale Salami, ya ce nadin Janar Musa babban abin alfahari ne ga kamfanin.
Ya ce:
“Aikin da Janar Musa ya yi wa Najeriya da jagorancin sa mai inganci za su kawo hangen nesa da ɗa’a cikin tsarinmu na gudanarwa.”
Martanin Janar Musa kan mukamin
Janar Christopher Musa ya bayyana godiyarsa bisa wannan dama da aka ba shi ya ce yana alfahari da kasancewarsa cikin hukumar da ke da burin gina alaka tsakanin nahiyoyi biyu.
Ya ce:
“Ina jin daɗin kasancewa cikin wannan tafiya mai hangen nesa. Kuma ina fatan amfani da kwarewata wajen ƙara wa wannan tafiya armashi.”
Midlothian Angel Network (Midlo) wata cibiyar saka jari ce mai hedikwata a Dallas, a jihar Texas da ke Amurka, tare da ofisoshi a Legas, Najeriya.

Source: Facebook
Cibiyar na da dukiya mai yawa tare da jimillar kadarori da suka kai sama da dalar Amurka biliyan 500, tana daga cikin manyan cibiyoyin saka jari a yankin Amurka da Afirka.
https://x.com/ZagazOlaMakama/status/1988630451544523066?s=20
Tsofaffin sojoji sun gargadi Wike
A wani labarin, kun ji cewa tsofaffi sojojin Najeriya sun gargadi ministan Abuja, Nyesom Wike kan rikici da wani soja a Abuja.
Tsohon shugaban sojojin kasan Najeriya, Tukur Yusuf Buratai na cikin tsofaffin jami'an da suka yi wa Wike martani.
Sun bukaci ministan Abuja da ya ba shugaban kasa hakuri tare da rundunar sojin Najeriya da ma jami'in da abin ya shafa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

