Tsofaffin Janar Sun Nuna Fushi kan Wike game da Rikici da Sojan Najeriya
- Tsofaffin hafsoshin soja sun nuna fushinsu kan rikicin da ya barke tsakanin ministan Abuja, Nyesom Wike, da wani soja, A. Yerima
- Ministan tsaro, Mohammed Badaru, ya ce an kafa kwamitin bincike kan lamarin, tare da tabbatar da kariya ga dakarun da ke aiki bisa doka
- Tsohon babban hafsan sojan ƙasa, Janar Tukur Buratai, da wasu manyan sojoji da suka yi ritaya sun ba Nyesom Wike rashin gaskiya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsofaffin Janar-janar na sojan Najeriya sun nuna matuƙar fushinsu bayan rikicin da ya barke tsakanin ministan Abuja, Nyesom Wike, da wani jami’in sojan ruwa mai suna A. Yerima.
Rikicin, wanda ya faru a ranar 11, Nuwamba, 2025, ya janyo ce-ce-ku-ce sosai bayan wani bidiyo da ya nuna yadda Wike ya yi muhawara da jami’in cikin fushi.

Kara karanta wannan
Ana batun matashin soja da Wike, Tinubu ya yi magana kan jarumtar sojojin Najeriya

Source: Facebook
Rahoton Punch ya nuna cewa manyan sojojin da suka yi ritaya sun yi Allah wadai da irin martanin da Wike ya yi wa sojan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buratai ya bukaci Wike ya nemi afuwa
Tsohon babban hafsan sojan ƙasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya bayyana cewa abin da Wike ya aikata ya sabawa ƙa’idar mutunta jami’an tsaro da kuma tsarin mulkin kasa.
A wani saƙo da ya wallafa a Facebook, Buratai ya ce:
“Fushin Wike ga jami’in soja a bainar jama’a ba wai kawai rashin ladabi ba ne, illa ce ga tsaron ƙasa da tsarin rundunar soja. Hakan neman wargaza tsarin umarni da mutuncin dakarun ƙasa ne.”
Ya kuma ce wannan dabi’a ta nuna rashin mutunta shugaban ƙasa a matsayin kwamandan rundunar soji, yana mai kira da a ɗauki matakin da ya dace.
Janar Aro ya gargadi Nyesom Wike
Wani tsohon Janar, Peter Aro, ya bayyana cewa lamarin ya nuna muhimmancin bin tsarin doka da umarni a mulkin dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan
DHQ: Hedkwatar tsaro ta wallafa kalmomi 3 bayan soja ya fatattaki Ministan Abuja, Wike
A cewarsa:
“Sojan yana kan aikinsa bisa umarnin tsohon babban hafsan sojojin ruwa. Ya kamata minista ya bi hanyoyin doka kamar rubuta wasika zuwa ga ministan tsaro ko zuwa kotu, maimakon rikici a bainar jama’a.”
Ya ƙara da cewa irin wannan lamari yana rage mutuncin gwamnati a idon duniya, kuma idan ba a yi Allah-wadai da shi ba, zai iya gurbata tunanin dakarun da ke kare ƙasar.

Source: Facebook
“Bai dace Wike ya yi haka ba” – Janar Adewinbi
Brigediya Janar Bashir Adewinbi (mai ritaya) ya bayyana cewa ba abin da za a yarda da shi ba ne minista ya yi faɗa da jami’in soja da ke bakin aiki.
Ya ce:
“Sojoji suna ƙarƙashin ikon shugaban ƙasa ne. Don haka duk wanda ya yi musu rashin kunya, tamkar ya yi wa shugaban ƙasa ne.”
Ministan tsaro ya bayyana matsayarsa
A wani labarin, ministan tsaro, Mohammed Badaru, ya jinjina wa jami’in ruwan bisa yadda ya nuna haƙuri yayin rikicinsa da Nyesom Wike.

Kara karanta wannan
Laftanal Yerima: Abin da muka sani game da sojan ruwa da ya fatattaki Wike a Abuja
Ya ce za su ci gaba da kare jami’an soji masu aiwatar da ayyuka bisa doka da tabbatar da cewa ba wanda zai cutu matuƙar yana yin aikinsa yadda ya kamata.
Badaru ya ƙara da cewa ana duba batun domin tabbatar da cewa adalci ya yi halinsa, tare da jan kunnen masu aiki a fannoni daban-daban da su mutunta tsarin rundunar soja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng