Zanga Zanga Ta Barke kan Rashin Tsaro a Katsina, an Samu Asarar Rayuka
- 'Yan bindiga sun addabi kauyen Danjanku da ke karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina da kai hare-hare
- Hare-haren na 'yan bindigan sun tilasta matasan yankin fitowa zanga-zanga domin nuna fushinsu kan matsalar rashin tsaro
- Sai dai, an samu asarar rayuka yayin da jami'an tsaro suka yi yunkurin tarwatsa matasan da suka fito zanga-zangar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Akalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu bayan wata zanga-zanga da ta barke a jihar Katsina.
Zanga-zangar ta auku ne cikin kauyukan Danjanku, Dantashi da Dayi da ke karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa zanga-zangar ta faru ne bayan sabon harin da ‘yan bindiga suka kai a daren ranar Litinin, 10 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
Harin 'yan bindigan ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya da sace wasu 17, duk da yarjejeniyar sulhu da aka kulla da su.
Mazauna yankin sun bayyana cewa harin na ranar na Litinin shi ne karo na uku cikin mako guda, lamarin da ya kai adadin mutanen da aka sace zuwa sama da 30 a yankunan da abin ya shafa.
Shaidu sun ce ‘yan bindigan sun farmaki kauyen Danjanku da misalin karfe 12:00 na dare, inda suka tsallaka katanga suka shiga gidaje, suka yi garkuwa da mutane sannan kuma suka kashe mutum ɗaya.
Matasa sun fito zanga-zanga
Saboda fusata kan lamarin, matasa sun fito da safiyar ranar Talata suna zanga-zanga, inda suka toshe babban titin Funtua–Katsina.
Matasan sun nuna ɓacin ransu kan hare-haren da kuma gazawar gwamnati wajen samar da tsaro.
Jaridar Vanguard ta ce zanga-zangar da ta fara cikin lumana ta rikide zuwa tashin hankali bayan da jami’an tsaro suka isa wajen domin tarwatsa su, inda ake zargin sun harbe mutane biyu har lahira tare da jikkata wasu mutum biyu.

Kara karanta wannan
Kogi: Jama'a sun barke da zanga zanga bayan 'yan bindiga sun jefa gawar tsohuwa a daji
Daga baya mazauna kauyukan Dantashi da Dayi suka shiga cikin zanga-zangar, inda suka toshe hanyoyi da kunna tayoyi domin nuna ɓacin rai kan tabarbarewar tsaro.
Hankula sun kwanta bayan aukuwar lamarin
An samu daidaituwar lamura bayan sarakunan gargajiya da dattawan yankin sun shiga tsakani.
Hakimin Danjanku, Alhaji Tanimu Almakiyayi, ya tabbatar da faruwar harin a ranar Talata, inda ya ce:
"Sun zo daren jiya, suka kashe mutum ɗaya daga cikin mutanenmu, kuma suka sace mutane da dama. Muna rayuwa cikin tsoro a nan.”

Source: Original
Wata majiyar tsaro ma ta tabbatar da lamarin, tana mai cewa:
"Yan bindigan sun farmaki Danjanku jiya da dare, suka sace mutane 17 tare da kashe mutum ɗaya.”
Mazauna yankin sun zargi sojojin da aka tura wajen da harbe masu zanga-zanga mutum biyu har lahira tare da jikkata wasu mutum biyu.
Kokarin da aka yi don jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Katsina bai yi nasara ba a lokacin da aka kammala hada wannan rahoto.
'Yan bindiga sun hallaka shugabannin al'umma
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun hallaka shugabannin al'umma yayin wani hari da suka kai a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

Kara karanta wannan
Sokoto: Gwamnati ta musanta sakaci kan harin 'yan bindiga, ta bayya yadda lamarin yake
'Yan bindigan sun kashe shugabannin al'ummar ne guda biyu a kauyen Doguwar Ɗorawa, kusa da Guga a karamar hukumar Bakori.
Majiyoyi sun bayyana cewa tattaro cewa yankar rago ‘yan bindigan suka yi wa mutanen biyu, ba harbinsu suka yi ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
