DSS Ta Tafi Kotu da Wanda Ya Nemi a Yi wa Tinubu Juyin Mulki a Najeriya

DSS Ta Tafi Kotu da Wanda Ya Nemi a Yi wa Tinubu Juyin Mulki a Najeriya

  • Hukumar DSS ta gurfanar da wani matashi mai shekaru 27, Innocent Onukwume, bisa zargin yin kira a yi juyin mulki
  • Ana zargin Onukwume da yin kalaman da ke iya tayar da hankalin jama’a da kawo tashin hankali a fadin Najeriya
  • An shigar da ƙarar ne a babbar kotun tarayya da ke Abuja, kuma ana sa ran za a fara shari’ar kafin karshen wannan mako

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar tsaron farin kaya DSS ta gurfanar da wani matashi dan jihar Rivers mai suna Innocent Chukwuemeka Onukwume a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa an gurfanar da shi ne bisa zargin yin kira ga juyin mulki da kuma ɓata suna ga gwamnati a kafar sada zumunta.

Kara karanta wannan

Barazanar Trump: Dalilin da ya sa Amurka ba za ta saka wa Najeriya takunkumi ba

Jami'an DSS
Wasu jami'an DSS a bakin aiki. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa lauya, A. M. Danalami ne ya shigar da ƙarar a madadin DSS a ranar 11, Nuwamba, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta bayyana cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a watan Oktoba na wannan shekarar.

A cewar takardar tuhumar, laifin da ake zargin Onukwume ya aikata ya sabawa tanadin dokar yanar gizo ta 2024.

Sakon juyin mulki da ake zargi ya wallafa

Tribune ta rahoto cewa DSS ta bayyana cewa Onukwume ya wallafa sakonni a shafinsa na X da ke kira ga kifar da gwamnati a Najeriya.

A cewar DSS, ya rubuta cewa:

“A Najeriya ana bukatar juyin mulki. A kori jam’iyyar APC, a dakatar da gwamnatin Najeriya, a shiga kungiyar AES, wannan ne kawai abin da ake bukata yanzu.”

Hukumar ta ce wannan kalami na iya tayar da hankalin jama’a da kawo cikas ga zaman lafiya a ƙasar, wanda ya sabawa doka.

Kara karanta wannan

Wuta ta tashi a kasuwar Singa da ke Kano da sassafe, shaguna sun kone

Shugaba Bola Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A wani sakon kuma, wanda ake tuhumar ya ce:

“Zai faru a ƙarshe. Sojoji suna bukatar goyon bayanku yanzu! Su kaɗai za su iya ceton wannan ƙasa.
"Wanda yake a Aso Rock ya sayar da ƙasar ga ƙasashen Yamma, su ne ke sarrafa bayanan sirri. Sojoji ne kaɗai za su iya dawo da tsarin ƙasa.”

DSS ta ce wannan kalaman na nuna ƙoƙarin tayar da fitina da ƙarfafa rashin gamsuwa da gwamnati, wanda ya sabawa dokokin ƙasa.

Tuhumar da DSS ke yi wa matashin

Hukumar DSS ta ce laifuffukan da ake tuhumar Onukwume da su suna ƙarƙashin tanadin sassan dokokin da ke hukunta duk wanda ya yi kira ko ya goyi bayan kifar da gwamnati.

A wani sashin tuhumar, DSS ta ce Onukwume ya kuma rubuta cewa:

“Dole ne Tinubu ya tafi, Dole jam’iyyar APC ta mutu kafin Najeriya ta samu walwala. Idan kana tunanin ƙuri’unka za su iya cire Tinubu, to kai wawa ne.”

Kara karanta wannan

Tirkashi: EFCC ta kafe hoton Timipre Sylva, ana neman tsohon gwamna ruwa a jallo

A cewar DSS, wannan kalami na nuna ƙoƙarin tada zaune tsaye da kuma raina tsarin dimokuraɗiyya a ƙasar.

Barazanar Trump: Matakin da Tinubu ya dauka

A wani labarin, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta ce gwamnatin Amurka ba za ta sa wa Najeriya takunkumi ba.

Daniel Bwala ya ce shugaba Bola Tinubu ya dauki mataki kan korafin da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi.

Bwala ya jaddada cewa Najeriya bata amince da cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi ba kamar yadda ake fada.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng