Tinubu, Gwamnoni, Sarkin Musulmi Za Su Hadu a Abuja, An Gano Dalilin Haduwarsu

Tinubu, Gwamnoni, Sarkin Musulmi Za Su Hadu a Abuja, An Gano Dalilin Haduwarsu

  • Shugaba Bola Tinubu, gwamnoni da ministoci za su halarci taron Editoci na Najeriya karo na 21 wanda za a gudanar a Abuja
  • Taron da kungiyar NGE ta shirya zai tattaro editoci fiye da 500, masu jaridu, jami’an diflomasiyya da kuma masana
  • An rahoto cewa Taken taron editocin na bana shi ne “Mulkin dimokuradiyya da ci gaban kasa: Rawar da editoci ke takawa”

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da gwamnoni, ministoci da fitattun ‘yan jarida, za su halarci taron Editocin Najeriya karo na 21.

Za a gudanar da taron masu tace labaran ne a Cibiyar Taron Fadar Shugaban Kasa, Aso Villa, Abuja, daga Laraba, 12 ga Nuwamba, 2025.

Tinubu, gwamnoni da manyan kasa za su halarci taron editoci a Abuja
Hoton Shugaba Bola Tinubu tare da gwamnonin Najeriya a Abuja. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da shugaban editocin Najeriya NGE, Eze Anaba, da skataren yada labarai, Onuoha Ukeh, suka fitar ranar Talata, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun tarwatsa yunkurin sace jami'ansu da limamin addini a Abuja

Sarkin Musulmi, gwamnoni za su dura Abuja

Sanarwar ta bayyana cewa taron zai tattaro editoci sama da 500 daga sassan kasar, da masu jaridu, jami’an diflomasiyya, masana da shugabannin kungiyoyin yada labarai.

Sanarwar ta bayyana cewa Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, da shugaban Arise News da ThisDay, Prince Nduka Obaigbena, za su jagoranci wasu zaman taron.

Haka kuma, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, zai gabatar da jawabin bude taron a matsayin mai gabatar da babban jawabin taro.

Sauran sun hada da Dauda Lawal (Zamfara), Caleb Mutfwang (Plateau), Abdullahi Sule (Nasarawa), da Abba Yusuf (Kano).

Manyan masana za su gabatar da makalu

Daga cikin mahalarta taron akwai tsohon gwamnan Ogun, Chief Segun Osoba, tsofaffin hadiman marigayi Shugaba Buhari — Femi Adesina da Garba Shehu, da kuma Dr. Ogbonnaya Orji na NEITI.

Za a kuma gudanar da tattaunawa kan rawar da editoci ke takawa wajen kare dimokuradiyya da hadin kan ƙasa, in ji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Ramat: Zanga zanga ta barke a majalisa don neman tabbatar da nadin shugaban NERC

A rana ta farko, Farfesa Awa Kalu (SAN) zai gabatar da makala kan "Rigingimun zabe da ingancin fannin shari'a: Nazari kan siyasa da doka."

Daga nan, Farfesa Sheriff Ibrahim daga jami’ar Abuja zai tattauna kan "Halin da kasa ke ciki: Garambawul ga tattalin arziki da siyasa a kasar da ke fuskantar jarabawa."

Abuja za ta yi cikar fari yayin da editocin Najeriya za su gudanar da taronsu na kasa
Hoton babbar alamar shiga birnin tarayya Abuja. Hoto: @iam_onismate
Source: Twitter

Zaman musayar ra’ayi da tattaunawa kan tsaro

A rana ta biyu, 13 ga Nuwamba, 2025 a cibiyar taro ta sojojin sama, tsohon shugaban hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor, zai gabatar da ta sa makalar, “Labarai, ta'addanci da tsaron kasa”.

Haka kuma, Farfesa Abiodun Adeniyi na jami'ar Baze zai gabatar da makala kan “Yadda aikin jarida ke sauyawa: Yaki da labaran karya, tangardar AI da rashin sahihancin bayanai."

A karshe, za a gudanar da zaman tattaunawa na musamman tsakanin editoci, jami’an gwamnati, da 'yan kasuwa domin inganta hadin kai tsakanin gwamnati da kafafen yada labarai.

Hafsan soja ya gana da Tinubu

A wani labarin, mun ruaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya karɓi rahoton tsaro daga Babban Hafsan Sojan Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu.

Kara karanta wannan

Minista ya fadawa 'yan Najeriya abin da za su yi bayan barazanar Donald Trump

Wannan shi ne karo na farko da shugaban ƙasa ke ganawar aiki da sabon hafsan sojoji tun bayan nadinsa da sauran takwarorinsa.

Janar Shaibu ya ce rahoton nasa ya ta’allaka ne kan cigaban da aka samu wajen yaƙi da ta’addanci da kuma yanayin tsaro a faɗin ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com