Barazanar Trump: Dalilin da Ya sa Amurka ba za Ta Saka wa Najeriya Takunkumi ba
- Fadar Shugaban kasa ta bayyana cewa Amurka ba za ta saka wa Najeriya takunkumi ba duk da barazanar shugaban kasa Donald Trump
- Himin Bola Tinubu, Daniel Bwala ya ce kowane irin takunkumi Amurka ta saka zai fi cutar da talakawa fiye da gwamnati kanta
- Bwala ya kara da cewa gwamnatin Najeriya ta dauki bayanin Trump da muhimmanci, tana kuma aiki don magance damuwar da aka nuna
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Fadar Shugaban kasa ta bayyana cewa ba ta ganin Amurka za ta ɗauki matakin takunkumi kan Najeriya duk da barazanar shugaban Amurka, Donald Trump.
Shugaba Donald Trump ya yi barazanar amfani da soja a Najeriya ne bayan zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi ba tare da dalili ba.

Kara karanta wannan
Hanyoyin da Tinubu da Nuhu Ribadu suka bullo wa barazanar harin Amurka sun fara jan hankali

Source: Twitter
Mai ba shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan yada labarai, Daniel Bwala, ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi a tashar Arise TV a ranar Litinin.
Ya ce duk wani takunkumi da Amurka za ta saka, zai fi yin illa ga jama’ar Najeriya maimakon gwamnati ko masu mulki.
Martanin Bwala kan barazanar Trump
Daniel Bwala ya ce irin wadannan takunkumi da kasashen waje ke kakabawa akan gwamnatoci ba su taɓa kawo sauyi ba, domin jama’a ne ke fama da sakamakon da suke haifarwa kai tsaye.
A cewarsa:
“Idan aka sanya wa Najeriya takunkumi, talakawa ne za su sha wahala, ba gwamnati ba. Shugaba Trump mutum ne mai furta abin da yake so, amma daga baya lamura su koma yadda suke.”
Ya kara da cewa irin wadannan maganganu daga shugabannin kasashen waje sukan kasance na siyasa ko nuna rashin jin dadi, amma ba lallai su kai ga aiwatar da wani mataki ba.
Matakin da gwamnatin Tinubu ta dauka
Daniel Bwala ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta fahimci sakon Trump kuma tana aiki don magance damuwar da aka nuna.

Source: Twitter
Leadership ta wallafa cewa Bwala ya ce:
“Gwamnatin Najeriya ta fahimci saƙon Trump sosai, kuma tana aiki a kai. Za mu fara ganin sakamako nan gaba kaɗan,”
Ya kara da cewa gwamnatin Tinubu tana da niyyar ci gaba da kare ‘yancin addini da tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’ummomi daban-daban a kasar.
Bwala ya ce Amurka za ta yi taka-tsantsan kafin ta ɗauki wani mataki da zai iya haifar da matsin tattalin arziki ga Najeriya.
Barazanar da Trump ya yi ga Najeriya
A baya, Trump ya taba bayyana cewa ya umurci sojojin Amurka su fara shiri kan yiwuwar daukar matakin soja a Najeriya idan gwamnatin kasar “ta ci gaba da bari ana kisan Kiristoci.”
Wannan furuci ya biyo bayan matakin da gwamnatin Trump ta dauka a baya na sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake saka ido a kansu, bisa zargin ake yi na cin zarafin mabiya addinin Kirista.
Gwamnatin Najeriya ta karyata ikirarin shugaba Trump tare da cewa rashin tsaron da kasar ke fama da shi bai ta'allaka ga wani addini daya ba, kuma tana kokarin shawo kan matsalar.
Asali: Legit.ng

