Nnamdi Kanu: Matsayar Tinubu kan Shari'ar Jagoran Kungiyar IPOB

Nnamdi Kanu: Matsayar Tinubu kan Shari'ar Jagoran Kungiyar IPOB

  • Ana ci gaba da kiraye-kiraye kan a saki jagoran haramtacciyar kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu
  • Hadimar shugaban kasa ta bayyana cewa lokaci bai yi ba da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai tsoma baki kan lamarin
  • Chioma Wesley ta nuna cewa Mai girma Tinubu ba zai ce komai ba kan shari'ar Nnamdi Kanu saboda lamarin yana gaban kotu

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Babbar hadimar shugaban kasa kan huldar jama'a (Kudu maso Gabas), Mrs. Chioma Wesley, ta bayyana matsayar Shugaba Bola Tinubu kan shari'ar Nnamdi Kanu.

Chioma Wesley ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ba zai yi wata magana game da shari’ar da ake yi wa jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ba saboda lamarin yana gaban kotu.

Shugaba Tinubu ba zai yi magana kan shari'ar Nnamdi Kanu ba
Shugaba Bola Tinubu da jagoran IPOB, Nnamdi Kanu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa ta bayyana haka ne a lokacin da ta ke magana da manema labarai a fadar shugaban kasa, da ke Aso Rock Villa, Abuja.

Kara karanta wannan

Matar shugaban APC ta fara gangamin tazarcen Tinubu, ta yi kira ga matan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ye matsayar Tinubu kan Nnamdi Kanu?

Ta yi magana ne bayan ita da wasu hadiman shugaban kasa daga yankuna daban-daban sun gabatar da rahotanni ga shugaban kasa a ranar Litinin, 10 ga watan Nuwamban 2025.

“Batun Nnamdi Kanu yana gaban kotu, kuma shugaban kasa ba zai iya yin wata magana a kai ba."
"Yana bin doka da oda. Don haka, a halin yanzu, za mu jira kotu ta yanke hukunci.”

- Chioma Wesley

Wannan furuci nata ya zo ne bayan kiraye-kirayen da suka sake karuwa daga yankin Kudu maso Gabas da ke neman a saki Nnamdi Kanu.

Tarihin shari'ar Nnamdi Kanu

Nnamdi Kanu, jagoran haramtacciyar kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), an kama shi ne a karon farko a shekarar 2015, sannan aka ba shi beli a 2017.

Daga bisani ya tsere inda ya bar kasar bayan dakarun sojoji sun gudanar da wani aiki a garinsa na Afaraukwu, jihar Abia.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da batun barazanar Trump, Tinubu ya gana da shugaban kasar Saliyo

An sake kama shi kuma aka dawo da shi Najeriya a watan Yunin 2021, kuma tun daga lokacin yana tsare a hannun hukumar DSS.

An shirya yanke hukunci a shari’ar da ake masa kan zargin ta’addanci a ranar 20 ga watan Nuwamba, 2025, bayan da ya ki kare kansa a karo na shida.

Shirye-shiryen ofishi hadimar Tinubu

Mrs. Wesley ta bayyana cewa ofishinta na Kudu maso Gabas ya kafa wani shiri domin samar da hanyar sadarwa tsakanin fadar shugaban Kasa da al’ummar yankin.

Shugaba Tinubu zai jira kotu kan shari'ar Nnamdi Kanu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook
“Mun fara aiki da kafa majalisar jama’a domin mu saurari ra’ayoyin al’umma game da manufofin shugaban kasa."
"Muna kai manufofin shugaban kasa zuwa ga jama'a, domin mutane su san abin da yake yi musu."

- Chioma Wesley

Nnamdi Kanu ya jero shaidu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu, ya jero mutanen da yake so su bada shaida kan shari'ar da ake yi masa.

Wannan mataki na Kanu ya biyo bayan ƙin amincewar kotu da karar da ya shigar don kalubalantar hurumin wani alkali kan ci gaba da shari’arsa.

Kara karanta wannan

A karon farko, Tinubu ya fadi abin da Najeriya ke yi kan barazanar Trump

Jagoran na kungiyar IPOB, ya sanar da alkalin kotun, mai shari’a James Omotosho cewa zai gabatar da shaidu 23.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng