Dambazau: ‘Yan Ta’adda Sun Mamaye Garuruwa, Suna Karɓar Haraji da Kafa Dokoki a Arewa

Dambazau: ‘Yan Ta’adda Sun Mamaye Garuruwa, Suna Karɓar Haraji da Kafa Dokoki a Arewa

  • Tsohon Ministan Cikin Gida, Janar Abdulrahman Dambazau mai ritaya ya ce ‘yan ta’adda sun mamaye wasu yankuna a Arewa
  • Ya bukaci gwamnonin Arewa su kafa ma’aikatar albarkatun ƙasa don rage talauci da rashin tsaro da ke mamaye shiyya
  • A jawabansu kan matsalar, Sarkin Musulmi da gwamnonin Nasarawa da Kebbi sun bukaci haɗin kai domin dawo da zaman lafiya a yankin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kebbi – Tsohon Ministan Cikin Gida, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau mai ritaya, ya bayyana damuwarsa kan tabarbarewar tsaro a Arewa.

Ya bayyana cewa a yanzu haka, an kai matakin da ‘yan bindiga da masu tayar da kayar baya suka karɓi ikon wasu yankuna, suna karɓar haraji da kafa dokoki.

Kara karanta wannan

Zabe ya bar baya da kura, an bindige kansila yayin jefa kuri'a a Anambra

Dambazau ya ce matsalar tsaro ta girmama a Arewa
Hoton Laftanar Janar AbdulRahman Bello Dambazau Hoto: AbdulRahman Ahmad
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Dambazau ya bayyana hakan ne a taron Media and Security Summit na farko da aka gudanar a Birnin Kebbi da ke Jihar Kebbi.

Dambazau ya koka kan girman matsalar tsaro

A taron mai taken barazana da matsalolin tsaron, Dambazau ya ce matsalar tsaro a Arewa ta haura fiye da shekaru 20 tana ci gaba da ta’azzara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

“Ana kashe mutane a masallatai a Katsina, Borno, Zamfara da Kano. Arewa ta yi fama da rikicin manoma da makiyaya, ta’addanci da satar mutane. Yanzu har wasu ‘yan ta’adda suna karɓar haraji daga al’umma kuma suna kafa dokoki."

Ya ƙara da cewa, dubunnan mutane sun mutu, miliyoyi sun rasa matsugunnai, manoma sun bar gonakinsu, kuma makiyaya sun rasa dabbobi saboda rashin kulawa daga hukumomi.

Kiran Dambazau, Sarkin a kan rashin tsaro

Dambazau ya shawarci gwamnonin Arewa su kafa Ma’aikatar Albarkatun Ƙasa, su haɗa kai da hukumomin tarayya wajen sarrafa albarkatun ƙasarsu.

Kara karanta wannan

'Yan majalisar Amurka sun taso Miyetti Allah a gaba kan zargin kisan kiristoci a Najeriya

Ya ce wananna za taimaka wajen ƙara samun kuɗin shiga da rage talauci, wanda a cewarsa shi ne tushen rashin tsaro.

Ya kuma bukace su dawo da mutuncin tsarin gargajiya, su inganta noma, su magance matsalar yara marasa zuwa makaranta, tare da samar da haɗin kai a cikin al’umma.

Dambazau ya bayyana cewa akwai bukatar a nemo bakin matsalar tsaro
Taswirar jihar Kebbi, inda aka gudanar da taron masu ruwa da tsaki a kan tsaro Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce:

“Fiye da kashi 70 cikin 100 na masu fama da talauci sakamakon rashin tsaro suna Arewa. Tsatsauran ra’ayin addini yana daga cikin manyan barazanar tsaro a yankin."

A nasa jawabin, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce tsaro aiki ne na kowa da kowa, yana mai jaddada cewa dole ne a tattauna domin nemo mafita.

Sarkin Musulmi ya ce:

“Ba haka muke ba a da. Idan muka haɗa kai, za mu iya gyara halin da ake ciki."

A nasa bangaren, Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce lokaci ya yi da Arewa za ta tashi tsaye don kawo ƙarshen rashin tsaro.

Shi kuma gwamnan da aka yi taron a jiharsa, Nasir Idris, ya ce taron zai taimaka wajen gano dalilan matsalar da kawo mafita domin samun sauki.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ba ku sani ba game da Zohran Mamdani, sabon magajin garin New York

Malamai sun shawarci Tinubu kan rashin tsaro

A baya, mun ruwaito cewa jagororin addinai daga bangarorin Musulunci da Kiristanci sun yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da ya ayyana ranar yi wa kasa addu'a.

Jagororin sun nemi a tsayar da ranar domin addu’a da azumi don neman taimakon Allah wajen kawo ƙarshen hare-haren ‘yan bindiga da sauran masu tada kayar baya.

. Buƙatar shugabannin addinin na zuwa ne lokacin da Shugaban Amurka, Donald Trump da ƴan majalisar ƙasar ke barazanar afka wa Najeriya saboda zargin kisan kiristoci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng