Zargin Kisan Kiristoci: Babachir Ya Fasa Kwai kan Rawar da Buhari da Tinubu Suka Taka

Zargin Kisan Kiristoci: Babachir Ya Fasa Kwai kan Rawar da Buhari da Tinubu Suka Taka

  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya yi tsokaci kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya
  • Babachir Lawal ya bayyana cewa tun da farko wasu wakilai na jam'iyyar APC suka nuki gari suka je Amurka don jawo hankalinta kan batun
  • Ya bayyana cewa yanzu abu mafi muhimmanci da ya kamata a maida hankali a kai, shi ne kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya yi magana kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya.

Babachir Lawal ya ce wakilan jam’iyyar APC, ciki har da Shugaba Bola Tinubu, su ne farkon wadanda suka kai korafi ga gwamnatin Amurka a wasu shekaru da suka gabata game da zargin kisan Kiristoci a Najeriya.

Babachir ya ce Buhari da Tinubu sun je Amurka kan kisan Kiristoci a Najeriya
Marigayi Muhammadu Buhari, Shugaba Bola Tinubu da Babachir Lawal Hoto: @MBuhari, @aonanuga1956, @Babachirlawal
Source: Twitter

Babachir Lawal ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Litinin, 10 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

"Ba don kiristoci ba ne," An jero abubuwa 3 da suka harzuka Amurka ta fara shirin kawo hari Najeriya

Kalamansa na zuwa ne a matsayin martani kan jawabin Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya ce ya umurci ma’aikatar tsaron Amurka ta shirya domin daukar mataki kan Najeriya saboda zargin kisan Kiristoci.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta musanta zargin, tana mai cewa matsalar tsaro na shafar kowane addini a kasar.

Me Babachir ya ce kan kisan Kiristoci?

“Trump na iya fadar gaskiya ko kuma ba haka ba, amma ku tuna cewa akwai wasu wakilai na APC da suka tafi Amurka a wancan lokacin don sanar da, ina ganin Obama ne a lokacin, cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya."
"A cikin wannan tawaga akwai Shugaba Tinubu, Buhari, da Rotimi Amaechi. Na ga hoton, har ma Tinubu ne yake zaune kusa da shugaban kasar a lokacin.”
“Sun tafi ne domin su yi kamun kafa wajen Amurkawa su gaskata cewa gwamnatin Goodluck Jonathan tana aiwatar da kisan kare-dangi a Najeriya.”

- Babachir Lawal

Kara karanta wannan

A karon farko, Tinubu ya fadi abin da Najeriya ke yi kan barazanar Trump

Babachir ya ba gwamnati shawara

Sai dai, Babachir Lawal ya ce yanzu abin da ya fi muhimmanci shi ne goyon bayan gwamnati ta tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, ba batun addini ba.

Babachir Lawal ya soki gwamnatin APC
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal Hoto: Babachir Lawal
Source: Facebook
“A manta da batun ana kisan kare-dangi ko ba a yi a Najeriya. Abin da muke so daga gwamnati shi ne ta tabbatar da tsaron rayukanmu da dukiyoyinmu, kawai hakan muke bukata daga gwamnati."

- Babachir Lawal

Tsohon SGF din ya kuma soki gwamnatin Tinubu, yana mai cewa bata nuna damuwa wajen magance matsalolin tsaro da rikice-rikicen addini a kasar nan ba.

Ya bayyana cewa gwamnatocin Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan sun fita kokari wajen daukar matakai don magance matsalar rashin tsaro a Najeriya​.

Babachir ya caccaki Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya caccaki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Babachir Lawal ya yi zargin cewa Shugaba Tinuhu bai damu ya magance matsalar rashin tsaron da ake fama da ita ba.

Kara karanta wannan

Trump: Sojojin Amurka sun tsara yadda za su kawo farmaki Najeriya

Tsohon sakatarem gwamnatin tarayyar ya ce gwamnatocin baya sun fi Tinubu kokari wajen magance matsalar rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng