Babachir Lawal Ya Taso Shugaba Tinubu a Gaba kan Matsalar Rashin Tsaro

Babachir Lawal Ya Taso Shugaba Tinubu a Gaba kan Matsalar Rashin Tsaro

  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya sake taso shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a gaba kan matsalar rashin tsaro
  • Babachir Lawal ya bayyana cewa gwamnatocin da suka gabata sun fi kokarin wajen ganin sun kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya
  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya kuma caccaki mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya zargi gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Tinubu da gazawa wajen magance matsalolin tsaro a kasar nan.

Babachir Lawal wanda ya yi aiki a karkashin marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba ta da niyyar magance matsalar tsaro.

Babachir Lawal ya ragargaji Shugaba Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal Hoto: Babachir Lawal, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Babachir Lawal ya bayyana hakan yayin da yake magana a shirin 'Politics Today' na Channels Tv.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi magana kan zaben Anambra, ya aika sako ga Gwamna Soludo

Me Babachir ya ce kan gwamnatin Tinubu?

Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya kwatanta gwamnatin Tinubu da ta tsofaffin shugabanni, Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari, yana mai cewa gwamnatocinsu sun fi gwamnatin yanzu.

“Tsofaffin gwamnatoci sun fi wannan, sun fi gaskiya, adalci, da niyyar yaki da cin hanci. A bangaren tsaro ma, Goodluck Jonathan ya yi kokari, Buhari ya yi nasa kokarin, amma wannan gwamnatin ba ta damu ba."

- Babachir Lawal

Ya ce kafin Tinubu ya hau mulki a watan Mayun 2023, jihar Adamawa (inda ya fito) ta kasance cikin kwanciyar hankali, amma yanzu tsaro ya tabarbare fiye da baya.

Babachir Lawal ya kuma soki mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, yana cewa bai ga wani abin kirki da ya yi a ofishinsa ba.

“Ban ga aikin da yake yi ba. Da na gani, zan faɗa. Idan na ga abin da yake yi, zan faɗa. Sojoji suna can suna mutuwa, akwai wadanda suke daga yankina, wasu sun dawo gawarwaki. Na san su.”

Kara karanta wannan

BoT: PDP ta dare gida 2, tsagin Abdulrahman ya kafa sabon kwamiti a gidan Wike

- Babachir Lawal

Ya ce sojojin Najeriya na mutuwa ne saboda tsarin da ya kamata ya taimaka musu ya gaza, inda ya misalta cewa ana tura sojoji da tsofaffin bindigogi yayin da ‘yan ta’adda ke amfani da manyan makamai.

“Kana tura soja da tsohuwar bindiga mai ɗaukar harsashi 20, amma makiyi yana da bindigar da ke iya harbi har zuwa kilomita ɗaya. Kana harbi sau ɗaya, bindigarka ta makale.”

- Babachir Lawal

Babachir ya soki gwamnatin Shugaba Tinubu
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal Hoto: Babachir Lawal
Source: Facebook

Da aka tambaye shi me ya sa bai gyara wannan matsala ba lokacin yana SGF, Babachir Lawal ya kare gwamnatin Buhari, yana mai cewa:

“A zamaninmu an sayi makamai masu kyau. Muna da shugaba soja wanda ya fahimci matsalar sosai. Ya yi abin kirki. Watakila shi (Tinubu) bai damu ya magance matsalar ba ne."

Tinubu ya taya Soludo murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi tsokaci kan zaben gwamnan da aka gudanar a jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Tinubu ya rantsar da sababbin ministoci, ya sha alwashi kan ta'addanci

Shugaba Tinubu ya taya Gwamna Chukwuma Soludo murna kan nasarar da ya samu a zaben gwamnan na ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamban 2025.

Ya bayyana cewa nasarar da Gwamna Soludo ya samu, alama ce da ke nuna cewa mutanen jihar sun gamsu da jagorancinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng