Zaben Anambra: Dan Takarar Jam'iyyar Labour Ya Barranta da Sakamakon Zaben Gwamna

Zaben Anambra: Dan Takarar Jam'iyyar Labour Ya Barranta da Sakamakon Zaben Gwamna

  • Moghalu ya ce zaben Anambra ba komai bane face farfajiyar sayen kuri’u da kuma kada kuri’un kananan yara
  • Ya zargi INEC da rashin tabbatar da amincin tsarin zaben da aka yi a ranar Asabar 8 ga watan Nuwamba
  • Ya bayyana cewa zai ɗauki mataki bayan ya karɓi cikakken rahoton wakilansa game da sahihancin zaben

Anambra, Najeriya – Dan takarar jam’iyyar Labour a zaɓen gwamnan Anambra da aka gudanar ranar 8 ga Nuwamba, 2025, Dr. George Moghalu, ya bayyana cewa bai amince da sakamakon da hukumar INEC ta fitar ba.

Ya kuma bayyana cewa, ayyana Gwamna Chukwuma Soludo na jam’iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen bai daidai bane.

A yayin da yake magana da manema labarai a ofishinsa da ke Nnewi ranar Lahadi, kasa da awanni shida bayan sanarwar sakamakon, Dr. Moghalu ya ce bai gamsu da yadda aka gudanar da zaɓen ba.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Dan takarar ADC ya gano lam'a a zabe, ya ce bai gamsu da sakamako ba

Ya zargi cewa an samu gurɓata da yawa, ciki har da sayen kuri’u da kuma ganin yara ƙanana na kada kuri’u a wasu rumfunan zaɓen jihar.

Dan takarar LP ya ce bai gamsu da sakamakon zabe ba
Dan takarar Labour ya ce an yi murdiya a zaben Anambra | Hoto: @MoghaluGeorge
Source: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Zaɓen ranar 8 ga Nuwamba, 2025 a jihar Anambra bai kai matsayin da ake tsammani ba.
“Na taba yin takara a baya, amma wannan zaɓen daban yake. Adadin sayen kuri’u abin damuwa ne.”

Yara kanana sun kada kuri’u a zaben Anambra

Ya ƙara da cewa akwai rahotannin yara da ke rike da katin zaɓe kuma aka bari suka kada kuri’a.

A kalamansa:

“An ga yara da ba su kai shekarunz abe ba suna riƙe da katin zaɓe kuma ana bari suna kada kuri’a.
“Wannan abu ne da ke nuna cewa akwai matsala wajen tabbatar da sahihancin tsarin zaɓen.”

An tauyewa jam’iyyar Labour ‘yanci, inji Moghalu

Moghalu ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin wakilansa sun kai rahoto cewa a wasu rumfunan zaɓe sunayen jam’iyyar Labour sun fito a takardar zaɓe ba tare da tambarin jam’iyyar ba, wanda hakan ya jawo rikicewa ga masu kada kuri’a, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Zabe ya bar baya da kura, an bindige kansila yayin jefa kuri'a a Anambra

Ya ce zai fitar da cikakken jawabi bayan ya karɓi rahoton da cikakken bayani daga wakilansa a fadin jihar.

Ya ce:

“Da zarar na karɓi cikakken rahoton zaɓen, za mu yi nazari sannan mu yanke shawarar matakin da za mu ɗauka. Amma abu ɗaya ya tabbata – na barranta daga sakamakon zaɓen nan baki ɗaya.”

Ya batun zuwa kotu?

Lokacin da aka tambaye shi ko zai kai ƙara kotu, Moghalu ya ce bai kamata ya yanke hukunci yanzu ba har sai ya gama duba rahotannin da ke hannunsa.

Dangane da zargin cewa wasu wakilan jam’iyyar Labour ba su kasance a wasu rumfunan zaɓe ba, ya ce wasu sun bar wurin saboda takaici da yadda ake tafiyar da zaɓen.

Ya kara da cewa:

“Wataƙila wasu daga cikinsu sun bar wurin ne saboda abin da suka gani na rashin gaskiya yayin kada kuri’u.”

Nwosu bai gamsu da sakamako ba

A gefe guda, dan takarar jam'iyyar ADC ya ce bai gamsu da sakamakon ba, inda ya zargi an yi sayen kuri'u a zaben.

Kara karanta wannan

Bidiyo: An ga 'yan sanda suna harba bindiga bayan Soludo ya lashe zaben Anambra

Ya kuma yi tsokaci kan yadda a hangensa ba haka ya kamata a gudanar da zaben ba, lamarin da ya dauki hankali.

Ya zuwa yanzu, ana taya dan takarar APGA murna, duk da akwai yiwuwar kalubalantar nasararsa a kotun zabe.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng