Sokoto: Gwamnati Ta Musanta Sakaci kan Harin 'Yan Bindiga, Ta Bayyana Yadda Lamarin Yake
- An zargi mahukunta da yin sakaci kan harin da 'yan bindiga suka kai a karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto
- Shugaban karamar hukumar Isa ya fito ya karyata zargin inda ya yi bayani kan abubuwan da suka faru kafin kawo harin
- Sharehu Abubakar Kamarawa ya kuma yabawa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu kan irin kokarin da yake yi wajen samar da tsaro
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Shugaban karamar hukumar Isa a jihar Sokoto, Hon. Sharehu Abubakar Kamarawa, ya karyata zargin sakaci da kin daukar mataki kan harin ’yan bindiga.
Harin da 'yan bindigan dai suka kai a kauyen Bargaja ya yi sanadiyyar mutuwar mutane shida da kuma sace wasu da dama.

Source: Facebook
Jaridar The Guardian ta ce hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da ya fitar da kansa a ranar Lahadi, 9 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me gwamnati ta ce kan harin 'yan bindiga?
Sharehu Abubakar Kamarawa ya bayyana zargin a matsayin karya da yaudara, yana mai cewa ba ya nuna hakikanin abin da ya faru.
Ya ce kafin harin, ya samu rahoton sirri kan motsin da ba a saba gani ba a yankin, kuma nan take majalisar karamar hukumar ta tura jami'an tsaro tare da sanar da hukumomin tsaro domin daukar mataki cikin gaggawa.
“An tura jami’an tsaro zuwa wurin da aka samu rahoton domin hana faruwar harin. Abin takaici, daga baya rahoton sirri ya nuna cewa ’yan bindigan sun kauce zuwa wata hanya daban da aka yi hasashen farko, wanda hakan ya haifar da wannan mummunan lamari."
- Sharehu Abubakar Kamarawa
Sharehu Abubakar Kamarawa ya kara da cewa an sauke kwamandan da ke kula da yankin da abin ya shafa saboda gazawa, kuma an nada sabon kwamanda, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da labarin.
Gwamnati na tallafawa jami'an tsaro
Ya tabbatar da cewa karamar hukumar tana ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da kayayyakin aiki, man fetur, da kudaden aiki, tare da tabbatar da cewa ’yan sa-kai suna samun kulawa da tallafi domin su ci gaba da hada kai da jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyi.
Shugaban karamar hukumar ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin Bargaja, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin jiha da ta karamar hukuma za su ci gaba da kokari wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
“Tsaro hakki ne na kowa. Maimakon yada labaran da ba su da tushe, ya kamata jama’a su rika ba hukumomin tsaro sahihan bayanai da za su taimaka musu wajen aikinsu.”
- Sharehu Abubakar Kamarawa

Source: Original
An yabawa gwamnan Sokoto
Ya kuma yaba wa Gwamna Ahmed Aliyu Sokoto saboda irin kokarin da yake wajen yaki da rashin tsaro a jihar, ciki har da rabon motoci da babura ga jami’an tsaro, dawo da alawus din aiki na wata-wata.
Ya kuma yaba masa kafa rundunar tsaro ta jihar Sokoto domin taimaka wa jami’an tsaro wajen kare rayukan jama’a.
'Yan ta'adda sun kashe jami'in Kwastam
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan ta'adda da ake zargin na Lakurawa ne sun kai hari kan sansanin jami'an hukumar Kwastam a Kebbi.
'Yan ta'addan sun hallaka jami'in kwastam tare da bankawa wata mota wuta a yayin harin da suka kai.
Harin na kara nuna matsalar rashin tsaron da ake fuskanta a jihar Kebbi musamman a yankunan da ke kan iyaka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


