Fasto Adeboye Ya Kawo Mafita, Ya Aika Sako ga Shugaba Tinubu kan Barazanar Amurka

Fasto Adeboye Ya Kawo Mafita, Ya Aika Sako ga Shugaba Tinubu kan Barazanar Amurka

  • Fasto Enoch Adeboye ya bayyana cewa tun da aka fara kashe kiristoci a Najeriya, ya ankarar da shugabannin kasar don daukar mataki
  • Babban limamin cocin RCCG ya shawarci Shugaba Tinubu ya dauki matakan gaggawa tun kafin Amurka ta fara kawo hari
  • A cewarsa, ya kamata Tinubu ya ba hafsoshin tsaro wa'adin watanni uku su kawar da yan ta'adda ko kuma su yi murabus

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babban limamin cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye, ya roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta daukar mataki kafin Amurka ta kawo farmaki Najeriya.

Fasto Adeboye ya bai wa Tinubu zabin matakan da ya kamata ya dauka tun da wuri domin gujewa farmakin da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar kawo wa.

Fasto Adeboye.
Hoton babban limamin cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye Hoto: Enoch Adeboye
Source: Facebook

Matakan da ya kamata Tinubu ya dauka

Kara karanta wannan

"Ba don kiristoci ba ne," An jero abubuwa 3 da suka harzuka Amurka ta fara shirin kawo hari Najeriya

The Cable ta tattaro cewa, na farko limamin cocin ya shawarci Tinubu ya shiga tattaunawa ta diflomasiyya da Shugaba Trump, kan zargin cin zarafin Kiristoci a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun farko, Trump ya umarci Ma’aikatar Tsaron Amurka da ta fara shirin “yiwuwar daukar matakin soji” a Najeriya.

Ya kuma gargaɗin gwamnatin Najeriya da ta kawo ƙarshen “kisan Kiristoci” da ya kira “mummunan abin kunya ga ƙasa.”

Sai dai gwamnatin Najeriya ta sha musanta wannan zargi, tana cewa ba a yin wani kisan kiyashi na addini a ƙasar.

Da yake jawabi a taron Holy Ghost Service na watan Nuwamba ranar Juma’a, Adeboye ya ce ya kamata Shugaba Tinubu ya gaggauta daukar mataki cikin hikima da diflomasiyya.

Adeboye ya nemi a lallaba Trump

Malamin cocin ya shawarci shugaban kasa ya nemi hanyar lallaba Trump ya ɗaga matakin da yake shirin ɗauka da tsawon kwanaki 100, rahoton Tribune Nigeria.

Faston ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta fallasa masu daukar nauyin ta’addanci da ‘yan tawaye a ƙasar, ba tare da la’akari da matsayin su ko tasirin su ba.

Kara karanta wannan

A karon farko, Tinubu ya fadi abin da Najeriya ke yi kan barazanar Trump

“Duk da shiru-shiru irin nawa, na kasance ina tattaunawa da dukkan shugabannin ƙasa tun lokacin da wannan matsala ta fara. Idan na je muka yi magana a sirrance, ina kuma zuwa na yi bakin kokarina ta bayan fage
"Amma iyaka mu ba shugaban kasa shawara, ba mu isa mu ba shi umarni ba. Da za a tambaye ni in ba da shawara, zan ce: gwamnatinmu ta tashi tsaye, ta yi amfani da diflomasiyya da hikima.
"A samo hanyar lallaba shugaban Amurka ya jinkirta matakinsa na tsawon kwanaki 100. Sannan a dawo gida, a umarci shugabannin tsaro su kawar da ‘yan ta’adda cikin kwanaki 90, idan ba haka ba su yi murabus.”

- In ji Fasto Enoch Adeboye.

Trump da abola Tinubu.
Hoton shugaban Amurka, Donald Trump da na Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: @realDonaldTrump, @OfficialABAT
Source: Getty Images

Rasha ta gargadi Amurka kan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin kasar Rasha ta ce tana sa ido sosai kan halin da Najeriya ke ciki bayan Amurka ta yi barazanar kai mata farmaki.

Rasha ta gargadi Amurka cewa duk wani mataki da za a ɗauka dole ne ya kasance bisa ka’idojin doka ta ƙasa da ƙasa.

Najeriya dai ta ƙaryata zargin Amurka cewa ana zaluntar Kiristoci a ƙasar, tana mai cewa babu wani tsarin gwamnati da ke nuna bambanci a addini.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262