Obaseki: Tsohon Gwamna Ya Bar Ofis da Bashin N600bn? An Ji Yadda Lamarin Yake
- Gwamnatin jihar Edo ta yi ikirarin cewa tsohon gwamna Godwin Obaseki ya tafi ya bar ta da dumbin bashi har na N600bn
- Tsohon gwamnan ya fito ya kalubalanci gwamnatin karkashin jagorancin Gwamna Monday Okpebholo, kan ikirarin da ta yi a kansa
- Obaseki ya bukaci gwamnatin da ta duba bayanai daga wajen hukumar DMO domin sanin ainihin bashin da aka biyo jihar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Edo - Tsohon gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya yi martani kan zargin cewa ya bar bashin Naira biliyan 600.
Godwin Obaseki ya karyata zargin barin bashin Naira biliyan 600, inda ya bukaci gwamnatin Monday Okpehbolo ta tabbatar da bayanan daga hukumar kula da bashi ta kasa (DMO).

Source: Twitter
Jaridar The Guardian ta tattaro cewa mai ba wa Obaseki shawara kan harkokin yada labarai, Crusoe Osagie, ne ya yi martani kan zargin.
Gwamnatin Edo ta zargi Obaseki da barin bashi
Kwamishinan yada labarai da tsare-tsare na jihar, Edo, Prince Kassim Afegbua, ya yi ikirarin cewa gwamnatin da ta gabata ta bar bashin Naira biliyan 600.
Prince Kassim Afegbua ya yi ikirarin ne a ranar Litinin, 3 ga watan Nuwamban 2025 a birnin Benin, babban birnin jihar Edo.
Wane martani Obaseki ya yi?
A martanin da ya yi, Crusoe Osagie ya kalubalanci gwamnatin yanzu da ta ziyarci ofishin DMO domin tabbatar da ko Edo ta taɓa ciwo irin wannan bashi.
Crusoe ya bayyana cewa babu wata gwamnati a kowanne mataki da za ta iya ciwo bashi ko shiga wata yarjejeniya ta kudi ba tare da amincewar DMO ba.
Ya bayyana cewa karyar da gwamnatin Gwamna Monday Okpebholo ke yadawa tana bata sunan jihar da kasar baki ɗaya, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar da labarin.
Ya ce irin wannan furuci yana nuna cewa jihar tana karkashin mutanen da ba su fahimci yadda ake tafiyar da gwamnati ba, inda ya bayyana zargin a matsayin tsantsagwaron karya.

Kara karanta wannan
Gwamna ya dakatar da sarkin da ake zargi yana daukar nauyin ta'addanci a Akwa Ibom
Game da shirin binciken cibiyar Museum of West African Art (MOWAA), Crusoe ya bayyana cewa cibiyar babbar kungiya ce ta duniya wadda ta shiga yarjejeniya da gwamnatin Edo bisa ka’ida.
Ya bayyana cewa duk bayanan yarjejeniyar da ke tsakanin MOWAA da gwamnatin Edo, suna cikin rahoton mika mulki.

Source: Facebook
"MOWAA babban wuri ne da ke samun kuɗi daga gwamnatin Jamus, Biritaniya, da Faransa don ci gaban ta. Shin kuna tunanin za a saka irin wannan hannun jarin a filin da ba gwamnati ta amince ta ba su shi ba?"
"Waɗannan mutanen suna fitowa ne kawai suna yada bayanai marasa tushe. A karshe, irin waɗannan maganganu sukan zama bayanan sirri da kasashen waje ke tarawa game da Najeriya.”
“Sannan hakan yana sa waɗannan kasashe su ɗauka cewa Najeriya ƙasa ce da ta gaza, wadda ba a tafiyar da ita bisa tsari.”
- Crusoe Osagie
Gwamnan Edo ya kori kwamishina
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Edo Monday Okpebholo, ya kori kwamishinan shari'a daga mukaminsa.
Gwamna Okpebholo bai bayyana wani dalili na korar kwamishinan ba wanda yana daya daga cikin wadanda ya fara rantsarwa a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan
Tsohon darektan DSS ya tsoratar da Najeriya a kan barazanar Trump, ya bada mafita
Tun da farko dai, an dade ana hasashen cewa Osagie zai rasa mukaminsa, tun bayan da aka bayyana sunayen sababbin kwamishinoni.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
