Yadda Mata ta Shafe Shekaru 40 Tana Bara, ta Mutu ta Bar Buhu 3 Cike da Kudi
- Rahoton da ya bayyana yadda wata mabaraciya ta shafe shekaru sama da 40 tana bara, amma ta gaza cin ko kadan daga kudinta
- An ruwaito cewa, an gano buhu uku cike da kudade mallakin Saleha, wacce aka ceta tar aba tare da amfani da sub a a rayuwarta
- Mazauna sun yi bayanin yadda matar ta shiga jinya, aka kwantar da ita asibitoci daban-daban kafin daga bisani rai ya yi halinsa
Sirajganj, Bangladesh – Saleha Begum wadda aka fi sani da Saleha Pagli, wata mata mai bara daga Sirajganj, ta rasu da yammacin Juma’a 24 ga watan Oktoba.
Rahoto ya ce ta rasu ne yayin da take jinya a asibitin Shaheed Ziaur Rahman Medical College da ke garin Bogura.
Marigayiyar, wadda matar marigayi Abdus Salam ce daga yankin Masumpur a Sirajganj, ta dade tana fama da rashin lafiya, inda aka ce ta daina fita bara saboda raunin jikinta, ta kuma koma zama a wani gida a yankin.

Source: UGC
An tsinci buhun kudi mallakin Saleha
A ranar 9 ga Oktoba, wasu mazauna yankin sun gano buhu gudu biyu cike da kudi a wani tsohon gidan gwamnati da aka bari babu kowa. Daga baya, a ranar 11 ga Oktoba, an sake gano wani buhun a wurin.
Jimillar kudin da aka kirga a buhunnan kudin ya kai kimanin Taka 1,74,080 kwatankwacin N2,086,453.248, kamar yadda jaridar The Financial Express ta ruwaito.
Mutanen yankin sun bayyana cewa Saleha Begum ta shafe kusan shekaru 40 tana bara amma bata cin kudin da take samu.
Da kudinta take rayuwar kunci
Mazauna da wadanda suka san ta sun ce rayuwarta ta kasance cikin kunci da wahala, tana mai adana taro da sisi da ta samu.
Lokacin da rashin lafiyarta ta tsananta, an fara jinyarta a asibitin yankin kafin daga bisani a kai ta asibitin Sirajganj Sadar da na North Bengal.
Daga nan aka tura ta asibitin Shaheed Ziaur Rahman Medical College, inda likitoci suka gano tana dauke da cutar kansar hanta, inji rahoton Daily Sun.
Ba sabon abu bane samun mutanen da suka ba da mamaki ba a duniya, musamman irin wadannan masu halin rashin amfani da dukiyarsu.
Cuta ta kai Saleha kabari
An yi binne Saleha da safiyar Asabar 25 ga watan Oktoba a makabartar Kandapara, bayan an kammala sallar jana’iza a ranar.
Mutanen yankin da dama sun yi tsokaci a kan rayuwarta, inda suka ce wannan duniya kowa zai bar ta babu komai, kamar yadda Saleha Begum ta bar duniya ta na da buhu uku cike da kudi amma babu abin da ta amfana da su.
Mace mafi tsawo a duniya
A wani labarin kuma, kundin tarihi na Guiness World Records ya tabbatar da cewa wata mata mai shekaru 24 'yar kasar Turkiyya ne mace mafi tsawo a duniya a halin yanzu.
A cewar Guiness World Records, Rumeysa Gelgi ta lashe kambun ne da tsawon 215.16cm (7ft 07in) kamar yadda ya zo a ruwayar BBC Pidgin.
An sake gwada tsawon Rumeysa a wannan shekarar, bayan an fara bata kambun mace yar kasa da shekara 19 a 2014, a lokacin da ta kai shekaru 18, tsawonta ya kai 215.16cm (7ft 0.7in) a lokacin.
Asali: Legit.ng

