Mata biyar da suka fi shahara a duniya

Mata biyar da suka fi shahara a duniya

Kamar yadda aka saba lokaci-lokaci, Legit.ng ta kan yi waiwaye ta binciko muku wasu muhimmanci mutane da suka shahara a duniya saboda wasu ayyuka da suka aikata wanda ya kawo wata muhimmiyar sauyi a rayuwar al'umma.

A yau mun kawo muku jerin mata biyar ne da su kafi shahara a duniya tare da hotunansu da kuma irin abubuwan da suka aikata da ya janyo musu kwarjini a tsakanin al'umma kamar yadda muka samu daga BBC.

1. Marie Curie (1867 - 1937)

Mata biyar da suka fi shahara a duniya
Mata biyar da suka fi shahara a duniya

Marie Sklodowska Curie ta shahara ne kan binciken sankara a wajen me turiri, ta bayar da gundun mawa wajen samar da injin daukar hoton X-ray.

A cewar wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da masu karanta mujallar BBC World History suka amsa, masaniyar kimiyya Marie Curie ta yi tasiri sosai a tarihin duniya.

Itace mace ta farko a duniya da ta fara lashe kyautar Nobel kuma Farfesa na farko a Jami'ar Paris.

2. Rosa Parks (1913 - 2005)

Mata biyar da suka fi shahara a duniya
Mata biyar da suka fi shahara a duniya

Rosa Louise McCauley Parks 'yar Amurka ce amma bakar fata wadda ta shahara saboda gwagwarmayar da tayi na samar wa bakar fata 'yanci.

An kama ta saboda ta ki bawa nai farar fata kujerarta a motar bas a 1955 a zamanin da ake ganiyar nuna banbancin lauyin fata a Amurka.

Wannan jarumtar da tayi yasa ake daukar ta a matsayin wadda ta kaddamar da neman 'yan a Amurka.

Tayi gwagwarmaya tare da mutane masu daraja kamar su Martin Luther King Jr da Edgar Nixon.

3. Emmeline Pankhurst (1858 - 1928)

Mata biyar da suka fi shahara a duniya
Mata biyar da suka fi shahara a duniya

Emmeline Pankhurst Goulden 'yar kasar Ingila ce wadda ta shara wajen gwagwarmayar siyasa.

Da ita aka kafa kungiyar Suffragettes, kungiyar dake neman baiwa mata 'yancin kada kuri'a zabe a wancan lokacin.

Jagorar mai farin jini, ita ta fara gwagwarmayar data kai ga samarwa mata 'yancin yin zabe duk da cewa wasu mutane da dama sun cacaki wasu akidunta da sukace sunyi tsauri da yawa.

Mujjalar Time ta ambaci Emmeline cikin mutane 100 da mafi muhimmanci a karni na 20.

4. Ada Lovelace (1815 - 1852)

Mata biyar da suka fi shahara a duniya
Mata biyar da suka fi shahara a duniya

Augusta Ada King-Noel 'yar asalin kasar Ingila ce wadda ta fito daga gidan sarauta. Ada kwarariya ce a fanin Lissafi da rubuce-rubuce.

Ana yi mata lakabi da Lovelace, mai hasashe kan kamfuta, itace ta fara tsara manhajar kwamfuta a duniya tare da wani shararen mai kirkira Charles Babbage suka kirkiro fasahar bibiyar alkaluma a shekarar 1880.

5. Rosalind Franklin (1920 - 1958)

Mata biyar da suka fi shahara a duniya
Mata biyar da suka fi shahara a duniya

Rosalind Elsie Franklin masaniyyar kimiyya ce 'yar kasar Ingila wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen fahimtar fasalin kwayoyin hallita na DNA da RNA.

Bincikenta kan kwayoyin hallita na DNA na daga cikin mafi muhimmancin ci gaban kimiyya na zamani a yanzu duk da cewa sai bayan rasuwarta masana suka fahimci irin gudunmawar data bayar.

A shekarar 1952 da ita aka kirkiri hoton da ya taimaka ake iya gano sakamakon kwayoyin hallita na DNA.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel