Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Martani bayan Trump Ya Yi Barazanar Kawo Hari a Najeriya
- Fadar shugaban kasa ta yi martani kan barazanar da Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi kan kawo hari Najeriya
- Hadimin Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa shugabannin kasashen biyu za su gana domin tattaunawa kan batun
- Daniel Bwala ya bayyana cewa dukkanin shugabannin biyu suna da manufa iri daya ta yaki da ta'addanci
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara na musamman kan sadarwa da manufofi, Daniel Bwala, ya yi tsokaci kan barazanar shugaban Amurka, Donald Trump.
Daniel Bwala ya bayyana cewa Shugaba Tinubu da Donald Trump za su gana a cikin ’yan kwanaki masu zuwa domin tattaunawa kan zarge-zargen da ake yi cewa ana gudanar da kisan gillar Kiristoci a Najeriya.

Source: Twitter
Hadimin na Shugaba Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Lauya a Amurka ya saba da Trump kan barazana ga Najeriya, ya fadi ciwon da ke damunsa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Trump ya yi barazana ga Najeriya
Maganganun Bwala sun biyo bayan kalaman Trump da suka tayar da muhawara, inda ya zargi gwamnatin Najeriya da rashin daukar mataki kan hare-haren da ake kaiwa Kiristoci.
Shugaban Amurka ya kuma yi barazanar kai farmaki a Najeriya don kashe ’yan ta’addan da ya ce suna kisan Kiristoci, tare da gargadin cewa Amurka na iya katse duk wata tallafi da taimako ga Najeriya.
A cewar Bwala, shugabannin biyu suna da manufa daya ta yaki da ta’addanci da ’yan tada kayar baya.
Ya tuna cewa Trump ya taba taimaka wa Najeriya ta hanyar amincewa da sayar da makamai, wadanda gwamnatin Tinubu ta yi amfani da su yadda ya kamata a yakin da take yi da ta’addanci.
“Shugaba Bola Tinubu da Shugaba Donald Trump suna da buri daya wajen yaki da ta’addanci da duk wata barazana ga bil’adama."
“Shugaba Trump ya taimaka matuka wajen amincewa da sayar da makamai ga Najeriya, kuma Shugaba Tinubu ya yi amfani da damar yadda ya kamata a yakin da ake yi da ta’addanci, kuma muna da sakamako mai gamsarwa don nuna hakan.”
- Daniel Bwala
Tinubu zai gana da Donald Trump
Game da muhawarar da ke cewa ’yan ta’adda a Najeriya suna kai hare-hare ne kan Kiristoci kawai ko dukkan addinai, Bwala ya ce batun zai kasance cikin jerin abubuwan da za a tattauna kuma a warware yayin ganawar shugabannin biyu.
Ya ce ganawar za a iya gudanar da ita a fadar shugaban kasa ta Abuja ko a fadar White House da ke birnin Washington.
“Dangane da bambance-bambancen ra’ayi kan ko ’yan ta’adda suna kai hari ga Kiristoci kawai ko kuma ga dukkan addinai, za a tattauna wannan batu a tsakanin shugabannin biyu a lokacin da za su gana a cikin ’yan kwanaki masu zuwa, ko dai a fadar shugaban kasa ko a White House."
- Daniel Bwala
Bashir Ahmad ya yi wa Sanatan Amurka martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon hadimin marigayi Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya yi wa Sanata Ted Cruz, martani kan yunkurin hana Shari'a da batanci a Najeriya.

Kara karanta wannan
Amurka ta gindayawa Najeriya sharadi bayan barazanar kawo hari kan zargin kisan kiristoci
Bashir Ahmad ya gayawa sanatan cewa zai iya kin Shari'a a kasarsa ta Amurka, amma ba ya tsoma baki a harkokin Najeriya ba.
Ya bayyana cewa Najeriya kasa ce mai 'yanci wadda bai kamata wani ya yi mata katsalandan cikin harkokinta ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng