Hana Shari'ar Musulunci a Najeriya: Bashir Ahmad Ya Yi Martani Mai Zafi kan Sanatan Amurka

Hana Shari'ar Musulunci a Najeriya: Bashir Ahmad Ya Yi Martani Mai Zafi kan Sanatan Amurka

  • Sanatan Amurka, Ted Cruz na shirin gabatar da kudiri domin sanya takunkumi ga masu aiwatar da dokokin Shari'a da batanci a Najeriya
  • Tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya yi martani mai zafi ga sanatan kan yunkurin da yake yi na gabatar da kudirin
  • Bashir Ahmad ya bayyana cewa aiwatarwa ko goyon bayan Shari'a ba laifi ba ne, kuma bai kamata sanatan ya tsoma baki kan harkokin Najeriya ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon mai taimaka wa shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya soki kudirin doka da Sanata Ted Cruz na Amurka ke shirin gabatarwa.

Kudirin na neman sanya takunkumi ga mutanen da suka taimaka wajen aiwatar da dokar Shari’a da batanci a Najeriya.

Bashir Ahmad ya soki Sanata Ted Cruz na Amurka
Bashir Ahmad da Sanata Ted Cruz na Amurka Hoto: @BashirAhmaad, @tedcruz
Source: Twitter

Bashir Ahmad ya soki yunkurin Sanata Ted Cruz ne a cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, 1 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Amurka ta gindayawa Najeriya sharadi bayan barazanar kawo hari kan zargin kisan kiristoci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane martani Bashir ya yi wa sanatan Amurka?

Bashir Ahmad ya bayyana cewa matakin sanatan ya nuna rashin girmama ikon Najeriya da tsarin dokokinta.

A cewarsa bai kamata a dauki aiwatarwa ko goyon bayan dokar Shari'a a matsayin laifi ba.

"Yanzu wani sanata a Amurka yana alfahari da cewa za su sanya takunkumi ga wadanda suka taimaka wajen aiwatar da Shari’a a Najeriya, sai ka ce dai aiwatarwa ko goyon bayan Shari’a laifi ne."
"Kana da ’yancin ka ka ki Shari’a a kasarka, amma ba ka da ikon ka shigo cikin al’amuranmu."
"Za mu kare ikon ƙasarmu da ’yancinmu na tsara dokokinmu da harkokinmu na cikin gida.”

- Bashir Ahmad

Ted Cruz na son hana Shari'a a Najeriya

Martanin Bashir Ahmad ta zo ne bayan da Sanata Ted Cruz ya bayyana cewa ya gabatar da kudirin doka a Majalisar Dattawan Amurka.

Ya ce ya gabatar da kudirin ne domin sanya takunkumi ga jami’an Najeriya da ake zargin suna aiwatar da dokokin batanci da Shari’a, musamman bayan zargin cewa ana cin zarafin Kiristoci a kasar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya maida martani ga Shugaban Amurka, Trump kan zargin kisan kiristoci a Najeriya

A cewar Ted Cruz, kudirin nasa zai karfafa matsayin gwamnatin Amurka wajen ɗaukar mataki kan waɗanda ake zargin suna da hannu a take hakkin addini a Najeriya, da kuma sanya musu takunkumin tafiye-tafiye da na kuɗi.

Ted Cruz zai gabatar da kudirin hana Shari'a a Najeriya
Sanata Ted Cruz mai neman hana aiwatar da dokar Shari'a a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wannan ya biyo bayan matakin tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda a ranar Juma’a ya ayyana Najeriya a matsayin “kasa mai babbar matsala” saboda abin da ya kira barazana ga Kiristanci.

Trump ya kuma yi zargin cewa ana kashe dubban Kiristoci a Najeriya ta hannun ’yan ta’addan addini, yana mai cewa lokaci ya yi da za a gudanar da bincike da kuma ɗaukar matakan siyasa domin dakatar da hakan.

Tinubu ya yi wa shugaban Amurka martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Donald Trump martani kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Najeriya kasa ce wadda ba ta lamuntar nuna wariya ko cin zarafin kowane addini.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Najeriya kasa ce mai mulkin dimokuradiyya wacce take bin kundin tsarin mulki da ke tabbatar da ’yancin addini ga kowa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng