Gwamnan Gombe Ya Kori Shugaban Babbar Hukuma, Ya Maye Gurbinsa da Sabo

Gwamnan Gombe Ya Kori Shugaban Babbar Hukuma, Ya Maye Gurbinsa da Sabo

  • Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya amince da sauyin shugabanci a hukumar ilmin bai daya ta jihar (SUBEB)
  • Inuwa Yahaya ya amince da korar Mr Babaji Babadidi daga mukamin shugabancin hukumar, inda ya maye gurbinsa da sabon shugaba nan take
  • Gwamnan ya godewa tsohon shugaban na hukumar SUBEB kan irin jagorancin da ya gudanar lokacin da yake kan kujerar shugabanci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya amince da sallamar Mr Babaji Babadidi daga matsayinsa na shugaban hukumar ilimin bai daya ta jihar Gombe (SUBEB).

Sallamar da Gwamna Inuwa ya yi wa shugaban hukumar na SUBEB za ta fara aiki ne daga ranar Jumma'a, 31 ga watan Oktoban 2025.

Gwamna Inuwa
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Hakan kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labaran gwamnan jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya sanya a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu da Birtaniya sun yi alhini da kwamishinan tsaro ya rasu a hadarin mota

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Inuwa ya yi sauyi a SUBEB

An yanke wannan matakin ne, wanda sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njoɗi ya sanar bisa ikon da aka ba gwamnan a karkashin sashe na 22 (4) na dokar hukumar ilimi ta jihar Gombe (da aka yiwa kwaskwarima) ta 2011.

A cewar sanarwar, Gwamna Inuwa Yahayan ya amince da naɗin Farfesa Esrom Toro Jokthan a matsayin sabon shugaban hukumar ilimin bai daya ta jihar Gombe nan take.

Ana sa ran Farfesa Jokthan, gogaggen masani kan harkokin ilimi, zai yi amfani da gogewa da basirarsa wajen ƙarfafa nasarorin da gwamnatin Inuwa Yahaya ta samu a ɓangaren ilimi a matakin farko.

Yayin da yake godewa Mista Babadidi, kan hidimar da ya yi wa jihar, Gwamna Inuwa Yahaya, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da yin gyare-gyare da inganta fannin ilimi wanda shine ginshiƙi mai muhimmanci a ajandarsa ta ci gaban tattalin arziki da gina jama'a.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya nada gwamnan Kwara da wasu gwamnoni 6 a mukamai na musamman

Gwamnan ya nuna kwarin gwiwar cewa sabon shugaban na SUBEB, zai yi amfani da kwarewarsa don haɓakawa da samar da ingantaccen ilimi daga tushe ga kowa kuma cikin sauki a jihar Gombe.

Gwamnan Gombe ya nada sabon shugaban hukumar SUBEB
Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Twitter

Karanta wasu labaran kan Gombe

Batun rashin sanya yara a makaranta a Gombe

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Gombe ta shirya sanya kafar wando daya da iyayen yaran da ba sa tura su zuwa makaranta.

Gwamnatin ta bayyana cewa za ta dauki matakin shari'a kan duk iyayen da aka samu da laifin rashin tura yaransu zuwa makaranta don su samu ilimi.

Shugaban hukumar SUBEB na jihar, Babaji Babadidi ya ce iyayen da suka sabawa dokar za su iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na watanni biyu a karkashin sashe na 19(2) na dokar SUBEB ta 2021.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng