EFCC Ta Kaddamar da Binciken Wadanda ake Zargi da Shirya Kifar da Gwamnatin Tinubu

EFCC Ta Kaddamar da Binciken Wadanda ake Zargi da Shirya Kifar da Gwamnatin Tinubu

  • An ce hukumomin EFCC da NFIU sun shiga binciken kuɗin da ake zargin sun tallafa wa yunkurin juyin mulki a Najeriya
  • Ana iya dakatar da asusun banki na wasu daga cikin wadanda ake zargi yayin da bincike ke cigaba da gudana
  • Rahotanni sun nuna cewa binciken ya shafi manyan sojoji da ‘yan kasuwa da ake zargin suna da hannu a lamarin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wani rahoto ya ce hukumar EFCC tare da NFIU sun shiga binciken yunkurin juyin mulki a Najeriya, domin gano hanyoyin kuɗin da ake zargin sun tallafa wa shirin.

An ruwaito cewa ana iya dakatar da asusun bankin wasu daga cikin waɗanda ake zargi yayin da binciken ke cigaba.

Jami'an hukuma EFCC.
Shugaban hukumar EFCC da wasu jami'ansa a bakin aiki. Hoto: EFCC Nigeria
Source: Facebook

Rahotanni daga jaridar Punch sun nuna cewa sojoji na aiki kafada da kafada da hukumomi wajen nazarin asusun bankuna da mu’amalar kuɗi na wadanda ake tuhuma.

Kara karanta wannan

Sojoji 2 sun tsallaka zuwa ketare yayin da ake nemansu kan zargin juyin mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu majiyoyi daban-daban sun ce EFCC da NFIU suna gudanar da bincike mai zurfi don gano tushen kuɗin, inda suke duba hada-hadar kudi da kuma gano asalin masu asusun.

Ana bincike kan kuɗin juyin mulki

Majiyoyi sun bayyana cewa binciken ya faɗaɗa zuwa ga abokan hulɗa da kasuwanci na manyan mutanen da ake zargi da hannu a shirin kifar da gwamnati.

Hakan na zuwa ne bayan zargin cewa an gano an fitar da sama da Naira biliyan 45 daga asusun NDDC zuwa wasu asusun da ake zargi suna da alaka da juyin mulkin.

A baya, Sahara Reporters ta ce an kama jami’an sojan Najeriya16 bisa zargin shirin kifar da gwamnatin Bola Tinubu, bayan soke bikin cikar ƙasa shekaru 65 da samun ‘yancin kai.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu a wani taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sai dai rundunar tsaron Najeriya ta karyata ikirarin da cewa soke faretin ba shi da alaka da juyin mulki.

Duk da hakan, jami’an tsaro sun mamaye gidan tsohon gwamnan jihar Bayelsa kuma tsohon minista, Timipre Sylva, da ke Abuja, inda suka kama wasu mutane a gidan.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fitar da gargadi kan yada labaran yi wa Tinubu juyin mulki

Aikin da EFCC da NFIU ke yi

A cewar majiyoyin soja, an dogaro da EFCC da NFIU wajen bin diddigin kuɗin da aka yi amfani da su a cikin shirin.

An ce waɗannan hukumomi za su tantance duk wata mu’amala ta kuɗi da ke da nasaba da wadanda ake zargi, domin gano masu hannu kai tsaye a lamarin.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, bai amsa kiran wayar da aka masa ba, haka nan kakakin NFIU, Aishatu Bantam, bata mayar da martani ba a ranar Alhamis.

Juyin mulki: Martanin fadar shugaban kasa

A wani labarin, mun kawo muku cewa fadar shugaban ƙasa ta nuna damuwa kan yadda rade-radin juyin mulki ke yawo a kafafen yaɗa labarai.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa irin waɗannan labaran da ba su da tushe na iya kawowa Najeriya matsala.

Onanuga ya yi kira ga 'yan jarida da su kasance masu haƙuri da bin doka, su daina yaɗa bayani kafin hukumomi su kammala bincike.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng