Kashim Shettima Ya Aika Sako ga Dattawan Arewa kan Batun Raba Najeriya
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya karbi bakuncin tawagar kungiyar dattawan Arewa mai suna Arewa Consultative Forum (ACF)
- Kashim Shettima ya tattauna muhimman batutuwan da suka shafi kasar nan tare da dattawan na Arewa a yayin ganarwar tasu
- Mataimakin shugaban kasan ya yi kira gare su da su nuna goyon baya ga gwamnatin Mai girma Bola Ahmed Tinubu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi kira ga kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) da ta ki yarda da masu tayar da fitina da ke kokarin raba Najeriya.
Kashim Shettima ya bukaci dattawan na Arewa da su tsaya tsayin daka wajen goyon bayan manufar “Renewed Hope” ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da ya karɓi tawagar ACF karkashin jagorancin shugaban kwamitin amintattu, Alhaji Bashir Dalhatu, a fadar shugaban Ƙasa, Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Shettima ya gayawa dattawan Arewa?
A cewar Shettima, babu lokaci mafi dacewa fiye da yanzu ga shugabannin Arewa su haɗa kai a matsayin ɗaya domin tallafa wa ƙoƙarin gwamnatin Tinubu na fitar da ƙasar nan daga matsin tattalin arziki da rikicin zamantakewa da ta tsinci kanta a ciki a baya.
Shettima ya shawarci ‘yan kungiyar da su ki yarda da makirce-makircen wasu masu tayar da fitina da ke son rugujewar kasar nan, rahoton jaridar The Punch ta zo da labarin.
Ya bayyana cewa wasu koke-koken suna fitowa ne daga neman adalci da daidaito, yayin da wasu ke fitowa daga son zuciya da neman cin gajiyar rikici don amfanin kai.
Wane aikin gwamnatin Tinubu ta sa a gaba?
Mataimakin shugaban kasan ya ce, babban aikin da ke gaban gwamnatin Tinubu shi ne ganowa da bambance tsakanin koke-koken gaskiya da na kwaɗayi.
"Sau da dama mun tabbatar cewa bambance-bambancenmu ne karfinmu. Bambancin kabila, addini, da wurin zama su ne tubalin ginin wannan gida na kaddara da muke rayuwa a ciki."
"Saboda haka dole mu ci gaba da kin amincewa da duk wani yunkuri na raba mu ko tayar mana da husuma. Makomar mu tana kan haɗin kai, kuma dole ne haɗin kai ya zama tubalin akidarmu.”
- Kashim Shettima

Source: Twitter
Game da zarge-zargen wariyar kabila da addini, Shettima ya tabbatar da cewa dukkan kabilu da addinai suna da ikon fada a ji a harkokin kasa a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, kuma ba wata kungiya ko yanki da za a nuna wa wariya.
Shettima ya ba budurwa kujerarsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban kasan Najeriya, Kashim Shettima, ya dora wata budurwa kan kujerarsa na rana daya.
Kashim Shettima ya ba wata yarinya mai suna Joy Ogah, damar zama mataimakiyar shugaban kasa na rana guda domin bayyana ra’ayinta kan batun ‘ya’ya mata.
A jawabin da ta gabatar bayan hawa kujerar, Joy Ogah ta jaddada bukatar gwamnati ta tabbatar da tsaro a makarantu, tare da samar da kayan tsaftace jiki kyauta ga ‘ya’ya mata.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

