Tinubu ya Cire Maryam Sanda da Wasu 'Yan Safarar Kwaya Cikin Wadanda ya Yiwa Afuwa

Tinubu ya Cire Maryam Sanda da Wasu 'Yan Safarar Kwaya Cikin Wadanda ya Yiwa Afuwa

  • Gwamnatin tarayya ta fitar da sabon jerin sunayen wadanda shugaban kasa ya yiwa afuwa a wannan shekarar
  • An cire mutum fiye da 50 daga jerin farko, ciki har da Maryam Sanda da aka gurfanar bisa lafin hallaka mijinta
  • Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya ce babu wanda aka saki tukuna, kuma akwai karin bayanai game da jerin sunayen

FCT, Abuja – Sunan Maryam Sanda, wadda kotu ta yanke wa hukuncin kisa bisa laifin kashe mijinta, bai bayyana a cikin sabon jerin fursunonin da suka samu afuwar shugaban ƙasa ba.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya fitar da wannan sabon jerin sunaye a ranar Laraba 29 ga watan Oktoban 2025.

Jaridar Daily Trust ta lura cewa an cire akalla sunaye 50 daga jerin farko da aka gabatar a baya da Maryam Sanda ke cikinsa.

An sake duba afuwar da aka yiwa Maryam Sanda
Yadda aka sake duba jerin wadanda Tinubu ya yiwa afuwa | Hoto: Imranmuhdz, InvestorBj3
Source: Twitter

Hukumar gwamnati ta sake duba jerin

A farkon Oktoba, Onanuga ya sanar cewa shugaban ƙasa ya yi afuwa ga wasu fursunoni, ciki har da waɗanda ke kan hukuncin kisa, da daurin rai da rai, bisa manyan laifuka irin su kasa, safarar miyagun ƙwayoyi, da hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta kashe mutum 100 a munanan hare haren da ta kai Gaza

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan mataki ne da ya haifar da cece-kuce daga jama’a da kungiyoyi masu kare haƙƙin ɗan adam.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce ba da afuwa ga waɗanda aka yanke wa hukunci kan manyan laifuka “na raunana amincewar jama’a da tsarin shari’a, kuma yana ƙarfafa masu aikata laifi.”

Shi ma Mallam Bolaji Abdullahi, kakakin jam’iyyar adawa ta ADC, ya bayyana wannan mataki a matsayin “cin zarafi ga ikon afuwar shugaban ƙasa”, yana mai cewa hakan abin kunya ne ga ƙasa.

An fara sake duba jerin saboda korafe-korafe

Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi, ya bayyana cewa kwamitin da yake shugabanta ne ya bada shawarar ba da afuwar, amma babu wanda aka saki tukuna.

Ya ce ana ci gaba da duba jerin sunayen saboda yadda jama’a suka nuna rashin amincewa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

A cikin wata sanarwa da Onanuga ya fitar a ranar Laraba, ya tabbatar da cewa an cire wasu sunaye daga jerin.

Kara karanta wannan

Yadda tankar mai ta kife a Neja, jama’a sun shiga matsanancin yanayi

A cewar sanarwar:

“Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da sakin wasu mutane bayan kammala tsarin amfani da ikon sa na ba da afuwa ga waɗanda aka yanke wa hukunci bisa wasu laifuka.
“Bayan tuntubar Majalisar Koli ta Ƙasa da kuma ra’ayoyin jama’a, shugaban ƙasa ya bayar da umarnin sake duba jerin farko da aka amince da shi, bisa tsarin ikon sa na ba da afuwa kamar yadda sashen 175(1)&(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka gyara) ya tanadar.
“Saboda haka, an cire waɗanda aka same su da manyan laifuka kamar garkuwa da mutane, safarar miyagun ƙwayoyi, sayar mutane, zamba, mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba, da makamantansu daga jerin. Wasu kuma an rage musu hukunci kawai.”

Dalilin da yasa aka sake duba jerin

Onanuga ya ƙara da cewa matakin ya zama dole saboda tsananin laifukan da aka aikata da kuma muhimmancin tsaron ƙasa, tare da la’akari da damuwar waɗanda abin ya shafa da kuma ƙarfafa jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

Hisbah ta soke shirin auren Mai Wushirya da 'Yar Guda, an ji dalili

Ya ce jerin waɗanda aka amince da su yanzu an mika shi ga Hukumar Kula da Kurkuku ta Najeriya domin aiwatar da shi bisa takardun da shugaban ƙasa ya sanyawa hannu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng