Isra'ila Ta Kashe Mutum 100 a Munanan Hare Haren da Ta kai Gaza
- Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutum 100 a Gaza sakamakon sababbin hare-haren Isra’ila, ciki har da wani ɗan jarida da matarsa
- Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ce jimillar mutanen da kasar Isra'ila ta kashewa Falasdinawa tun daga watan Oktoba 2023 ya haura 68,000
- Shugaba Donald Trump ya ce babu abin da zai hana yarjejeniyar zaman lafiya ci gaba, duk da cewa Isra'ila na kai hare-hare yankin Gaza
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Gaza – Akalla mutum 100 ne suka rasa rayukansu a sabon harin da sojojin Isra’ila suka kai yankin Gaza, ciki har da ɗan jarida Mohammed al-Munirawi da matarsa.
Rahotanni sun nuna cewa an kashe dan jaridar ne yayin da yake neman mafaka a wani tantin ‘yan gudun hijira a Nuseirat, a tsakiyar Gaza.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta ce hakan ya ƙara yawan ‘yan jarida da aka kashe tun farkon hare haren kasar Isra'ila zuwa 256.
Hukumar yaɗa labaran Gaza ta ce Isra’ila na ƙoƙarin murkushe duk wata muryar da ke bayyana laifuffuka da keta ‘yancin ɗan Adam a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa duk lokacin da Isra’ila ta kai hari, ‘yan jaridar Falasɗinu kan zama cikin barazana sosai, domin ana kai musu hari kai-tsaye.
Isra'ila ta kai hari Gaza bayan sulhu
Ma’aikatar lafiyar Gaza ta bayyana cewa hare-haren da Isra’ila ta kai tun daren jiya sun kashe aƙalla Falasɗinu 104, ciki har da yara 46, yayin da wasu 253 suka jikkata.
Tun bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 10 ga Oktoba, akalla Falasɗinu 211 aka kashe, yayin da aka gano gawawwakin mutane 482, inji ma’aikatar.
Ta kuma bayyana cewa, tun daga watan Oktoban 2023 zuwa yanzu, Isra’ila ta kashe mutane 68,643 tare da raunata fiye da 170,000.
An bayyana cewa lamarin na nuna ci gaba da tsanantan tashin hankali duk da yarjejeniyar zaman lafiya da ake magana akai.
'Yan Isra'ila sun kona motocin Falasdinawa
Wasu ‘yan mamaya na Isra’ila sun ƙona motoci biyu mallakar Falasɗinu a garin Surif, Arewa maso yammacin Hebron, a yankin da Isra’ila ke mamaya a Yammacin Kogin Jordan.
Haka kuma, a safiyar yau, wasu ‘yan mamaya sun sake ƙona motocin Falasɗinu a ƙauyen Atara, Arewa da Ramallah, abin da ke ƙara tayar da jijiyoyin wuya a yankin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa irin waɗannan hare-hare na faruwa a idon jami’an tsaron Isra’ila ba tare da an ɗauki matakin hana su ba.
Trump ya dage cewa zaman lafiya zai dore
A gefe guda, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa babu abin da zai kawo cikas ga yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi tsakanin Isra’ila da Hamas.

Source: Getty Images
Rahoton Yahoo News ya ce kalamansa sun ci karo da gaskiyar abin da ke faruwa, domin a daidai lokacin da yake magana, sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare Gaza.
Iran ta yi magana kan kashe-kashe a Gaza
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Iran ta yi Allah wadai da hare haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza.
Ayatullah Ali Khamenei ya kira Amurka da 'yar ta'adda kan cigaba da goyon bayan kasar Isra'ila a kan Falasdinawa.
Khamenei ya kara da cewa gwamnatin Amurka mafarki take game da cewa ta lalata cibiyar nukiliyar Iran a harin da ta kai.
Asali: Legit.ng


