1 cikin 6: Majalisar Tarayya ta Amince da Kafa Sabuwar Jiha a Najeriya

1 cikin 6: Majalisar Tarayya ta Amince da Kafa Sabuwar Jiha a Najeriya

  • An yi nasarar kai wa ga matsaya kan kafa sabuwar jiha a Najeriya, a yankin kudancin kasar da ke da jihohi biyar
  • Sai dai, an tike a inda ake yanke shawarin wacce daga cikin garuruwan da aka gabatar za a zaba don zama jiha
  • Baya ga yankin Kudu, ana ta fafutukar kafa wasu jihohin a Najeriya a yankin Arewa, sai dai har yanzu ba a kai ga nasara ba

FCT, Abuja - Majalisar Tarayya ta amince da kafa sabuwar jiha ta shida a yankin Kudu maso Gabas, matakin da ya tayar da muhawara a tsakanin ‘yan siyasa da mazauna yankin kan wace daga cikin jihohin da aka gabatar za a zaba a ƙarshe.

Bayan amincewar majalisar, an gabatar da shawarwari guda shida da za a duba kafin zaɓar ɗaya daga cikinsu, waɗanda suka haɗa da Orashi, Orlu, Anioma, Etiti, Aba, da Adada.

Za a kirkiri sabuwar jiha a Kudancin Najeriya
Yadda ake kokarin kafa sabuwar jiha a Najeriya | Hoto: NASS/IgboFestival
Source: Twitter

Jihohin da ake ba da shawarar kafa su a Kudu maso Gabas

Kara karanta wannan

Yadda tankar mai ta kife a Neja, jama’a sun shiga matsanancin yanayi

Waɗannan shawarwari suna wakiltar bambancin tarihi, al’adu da tsarin gudanarwa a tsakanin al’ummomin yankin Kudu maso Gabas da makwabtansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

  • Jihar Orashi: Ana son a ƙirkire ta daga sassan jihohin Anambra, Imo, da Rivers, kuma tana da muhimmanci wajen haɗa Kudu maso Gabas da yankin Kudu maso Kudu.
  • Jihar Orlu: Za a kirkiro ta ne gaba ɗaya daga yankin Kudu maso Gabas, kuma ‘yan yankin sun dade suna fafutukar ganin an kafa ta.
  • Jihar Anioma: Itama tana cikin yankin Kudu maso Gabas, ana ganin kafa ta zai haɗa al’ummomi masu ɗaure da juna ta fuskar kabila da al’ada.
  • Jihar Etiti: Wannan shawara ce da ke neman haɗa al’ummomin tsakiyar yankin Kudu maso Gabas domin inganta tsarin gudanarwa.
  • Jihar Aba: Ta samo sunanta daga birnin kasuwanci na Aba, kuma ana kallon ta a matsayin hanya ta ƙarfafa ci gaban tattalin arziki a yankin.
  • Jihar Adada: Ana shirin kirkiro ta daga Jihar Enugu, inda ake ganin kafa ta zai ƙara wa al’ummomin arewacin Enugu wakilci da tasiri a siyasa.

Kara karanta wannan

An gano daloli, motoci da alfarma da Tinubu ya ware wa korarrun hafsoshin tsaro

Dalilin kafa sabuwar jiha

Wannan mataki na Majalisar Tarayya wani babban ci gaba ne wajen daidaita rabon jihohi a tsakanin yankunan siyasa guda shida da ke ƙasar nan.

A halin yanzu, Kudu maso Gabas ce kaɗai ke da jihohi biyar, yayin da sauran yankuna ke da shida ko fiye. Masana sun bayyana cewa ƙirƙiro sabuwar jiha zai ƙara wa yankin damar samun wakilci da rabo a cikin ƙasar.

Tasirin siyasa da tattaunawar da ke gudana

Duk da cewa zaɓin ƙarshe na jiha ɗaya daga cikin shawarwarin zai bukaci karin matakai na doka da kuma amincewar shugaban ƙasa, wannan shawarar ta riga ta jawo hankalin shugabanni, kungiyoyin farar hula da mazauna yankin.

Masana harkokin siyasa sun ce sakamakon wannan shiri zai iya sauya taswirar siyasar Kudu maso Gabas gaba ɗaya, tare da tasiri a wajen raba mukaman gwamnati da wakilci a majalisu nan gaba.

Yayin da tattaunawa ke ci gaba, ana sa ran shugabanni da ‘yan siyasa daga yankin za su ƙara ƙaimi wajen neman goyon bayan kafa jiharsu ta mafarki.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Majalisa ta amince da kirkirar karin jiha 1 a Najeriya

A cewar majalisar, dukkan shawarwarin jihohi guda shida sun tsallake karatu na biyu a gaban majalisar, yayin da ake jiran matakin gaba wanda zai bayyana wace daga cikinsu za ta zama sabon jihar Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng