Yadda Tankar Mai ta Kife a Neja, Jama’a Sun Shiga Matsanancin Yanayi

Yadda Tankar Mai ta Kife a Neja, Jama’a Sun Shiga Matsanancin Yanayi

  • An samu hadarin tankar mai a jihar Neja, lamarin da ya dagawa mazauna yankin Lapai hankali a ranar Lahadi
  • Rahoto ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu jami’ai a hukumomi daban-daban suna nan suna aikin tabbatar da tsaro
  • Ana yawan samun hadurran manyan motoci a Najeriya, wannan na da nasaba da yaddaa titunan kasar ke lalacewa

Lapai, Jihar Neja - Wata tanka mai ɗauke da man fetur ta kife a kan hanyar Lambata-Lapai-Agaie da ke Jihar Neja, lamarin da ya haifar da tashin hankali a tsakanin mazauna yankin.

Binciken ya nuna cewa tankar, wanda ta tashi daga Legos zuwa Kano, ta kife ne da safiyar Lahadi a ƙauyen Takalafiya, da ke cikin karamar hukumar Lapai ta jihar Neja.

Kara karanta wannan

Fadar Vatican da kanta ta tsage gaskiya kan zargin kisan Kiristoci, ta yi gargadi

Wani mazaunin garin Lapai, Mallam Mahmud Abubakar, ya shaida wa Daily Trust ta wayar tarho cewa wurin da tankar ta kife na kusan kilomita biyu ne kacal daga tsakiyar garin Lapai.

Tankar mai ta kife a Lapai, Neja
Yadda aka kawo dauki bayan kifewar tankar mai | Hotuna: @connect_bida
Source: Twitter

Dalilin kifewar tankar mai a Neja

Ya bayyana cewa wurin da tankar ta kife yana daga cikin sassan titin da aka gyara kwanan nan a ƙarƙashin shirin gyaran tituna na kamfanin NNPCL, amma cikin ɗan kankanin lokaci titin ya fara lalacewa.

A cewar Mahmud:

“Wurin nan da tankar ta kife an gyara shi ba da jimawa ba a cikin aikin NNPCL, amma yanzu ya fara lalacewa, shi ne ya jawo wannan hatsari.”

A wata majiyar kuma, Mohammed Hassan Sonmaji, ya ce gaggawar da sashen kashe gobara na Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBUL) tare da jami’an NSCDC suka yi, ita ce ta taimaka wajen kauce wa mummunan bala’i.

Kara karanta wannan

Kano: Hisbah ta dakile shirin auren jinsi, an cafke kusan mutum 30

A cewarsa:

“Da ba a samu taimakon nan da wuri ba, da hatsarin nan ya iya zama bala’i mai girma, domin tankar cike rake da mai.”

Jami’an tsaro sun kawo daukin gaggawa

Ya kara da cewa jami’an Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas (NUPENG) reshen Lapai, sun isa wurin don taimakawa wajen sarrafa yanayin da abin ya faru.

Ya ce:

“Jami’an NUPENG sun kawo taimako domin a kwashe man da ya zube da kuma hana yaduwar haɗari.”

Rahotanni sun ce an tattara man da ya zube cikin ganguna domin kauce wa asara da kuma kare muhalli daga barna.

Hukumar Neja ta yi magana kan hadarin

Da aka tuntubi Dr. Ibrahim Audu Hussaini, darektan yada labarai da harkokin musamman na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), ya tabbatar da cewa babu abin da ya kamata a tayar da hankali a kai.

Kara karanta wannan

Daliban jami'a za su yi karatu kyauta saboda tallafin gwamna Umaru Bago

A kalamansa:

“Babu abin da ya kamata a damu da shi, tankar bata tashi da wuta ba. Motocin kashe gobara na jami’ar IBB Lapai suna wurin suna jiran ko wani abu zai faru.”

Ya kara da cewa jami’an tsaro ma sun isa wurin don tabbatar da cewa ba a samu wata matsala ko lalata dukiya ba.

Lamarin ya jawo cunkoson ababen hawa na ɗan lokaci a kan hanyar, yayin da jami’an tsaro suka ci gaba da tsare wurin domin kare rayuka da dukiyoyi.

An shiga fargaba a Neja bayan da tankar mai ta kife a Lapai

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng