An Barke da Murna da Farashin Shinkafa Ya Yi Kasa Sosai a Kasuwanni, an Gano Dalili

An Barke da Murna da Farashin Shinkafa Ya Yi Kasa Sosai a Kasuwanni, an Gano Dalili

  • Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa farashin shinkafa ya fadi sosai a wasu kasuwannin Lagos
  • ‘Yan kasuwa sun koka kan asarar da suka yi, suna cewa sun sayi shinkafa da tsada amma yanzu suna sayarwa da araha
  • Masana sun ce bude iyakoki da karin amfanin gona daga Arewa ne ya haifar da saukar farashin, amma farashin na iya tashi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Farashin shinkafa ya fadi sosai a kasuwannin jihar Lagos, bayan da aka samu karin shigo da ita daga kasashe makwabta, wanda hakan ya rage wa masu amfani da ita farashi.

Sai dai, ‘yan kasuwa sun nuna damuwa kan yadda wannan saukar farashin ke rage musu riba da kuma barazana ga dorewar harkokinsu na kasuwanci.

Farashin shinkafa ya fadi a kasuwa
Shugaba Bola Tinubu ya yi albishir kan farashin kaya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Farashin shinakafa a kasuwannin Lagos

Kara karanta wannan

An gano daloli, motoci da alfarma da Tinubu ya ware wa korarrun hafsoshin tsaro

Rahoton Daly Trust ya nuna cewa buhun shinkafa mai kilo 50 yanzu yana tsakanin ₦55,000 zuwa ₦70,000 a wasu kasuwanni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wasu manyan kasuwanni kamar Oyingbo, Arena (Oshodi), Festac Town da Mile 12, shinkafar gida da ake sayarwa ₦85,000 a watan Janairu yanzu tana tsakanin ₦60,000 da ₦70,000.

Ita kuwa shinkafar waje, da ta kai ₦95,000 a farkon shekara, yanzu tana tsakanin ₦65,000 da ₦75,000, gwargwadon inda ake sayarwa.

A kasuwar Arena, wata mai shinkafa, Mrs Precious Okoro, ta ce wannan saukar farashin ya jefa ‘yan kasuwa cikin asara mai tsanani.

Ta ce:

“Na sayi buhuna da ₦85,000, yanzu sai in sayar da ₦65,000. Asara muke yi.
“Shinkafa ba ta lalacewa da wuri, amma idan farashi ya fadi haka, kudinmu yana makale"

A kasuwar FESTAC Town, wata yar kasuwa, Mrs Edith Nwaruh, ta ce irin shinkafar 'Pretty Lady' tana ₦57,000, Mama Africa ₦62,000, Mama Gold ₦67,000, yayin da Big Bull Premium ke ₦73,000.

Ta bayyana cewa farashin ya fara sauka tun watan Agusta, bayan karin girbi daga Arewa da kuma karin shigo da shinkafa ta kasashen waje.

Kara karanta wannan

Jagororin PDP sun rabu a kan bai wa turaki shugabancin jam'iyya

Ta ce:

“Yanzu kasuwa ta cika da shinkafa, hakan yasa farashi ya sauka."
Farashin shinakafa ya yi kasa a Lagos
Shugaban kasa, Bola Tinubu yayin addu'a a masallaci. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Tsammanin da yan kasuwar shinkafa ke yi

A kasuwar Mile 12, wani dan kasuwa, Mr Odion Michael, ya ce “masu saye suna farin ciki, amma mu ‘yan kasuwa muna kuka.” Ya bukaci gwamnati ta tabbatar da daidaiton farashi don a samu damar tsara kasuwanci.

Wani manomin shinkafa da bai so a bayyana sunansa ba, ya danganta saukar farashin da bude iyakokin kasa, wanda ya kawo karin shigo da shinkafa daga kasashe makwabta.

Sai dai ya gargadi cewa saukar farashin ba zai dade ba, yana iya tashi kafin karshen shekara idan an samu karancin kayayyaki ko rashin daidaiton kasuwa.

Gwanabtu ta magantu kan farashin abinci

Kun ji cewa Fadar shugaban kasa ta ce an samu ragin farashin kayan abinci da ya kai tsakanin kashi 45 zuwa 52 cikin 100 a faɗin ƙasar nan.

Ta ce manufofin tattalin arzikin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne suka taimaka wajen inganta samar da abinci da rage farashi.

Kara karanta wannan

Farashin buhun shinkafa, masara, wake, ya ruguzo kasa a kasuwannin Abuja

Gwamnati na ganin saukar farashin a matsayin tabbaci na cigaban tattalin arziki da dorewar wadata ga ‘yan ƙasa baki daya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.