Abu Ya Girma: Majalisa Ta Amince da Kirkirar Jihohi 6 a Najeriya
- Akwai yiwuwar jihohin da ake a Najeriya su kara daga guda 36 zuwa 42 bayan an amince da kirkiro sababbi
- Kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa da majalisar wakilai ya amince da kirkiro.karin jihohi guda shida
- Amincewar na zuwa ne bayan kwamitin ya duba bukatu 55 masu neman a kirkiro karin jihohi a Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Kwamitin haɗin gwiwa na majalisar dattawa da majalisar wakilai kan sake duba kundin tsarin mulki ya amince da kirkirar jihohi a Najeriya.
Kwamitin ya amince da kirkiro karin jihohi guda shida a kasar nan.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce hakan na ɗaya daga cikin manyan matsayoyin da aka cimma a karshen taron bita na kwanaki biyu da aka gudanar a Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da taron ne karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da kuma mataimakin shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Benjamin Kalu.
An amince a kirkiro jihohi shida
A yayin taron, kwamitin ya tattauna kan kudirori 69, bukatu 55 na kirkirar jihohi, bukatu biyu na gyaran iyaka, da bukatu 278 na kirkirar kananan hukumomi.
Bayan la’akari da bukatun kirkirar jihohi 55 a ranar Asabar, kwamitin haɗin gwiwa ya yanke shawarar amincewa da karin kirkirar jihohi shida a kasar nan.
Idan wannan mataki ya samu amincewa, adadin jihohi a Najeriya zai karu daga 36 zuwa 42.
Amincewar na nufin za a kirkiri jiha guda ɗaya daga kowane yanki guda shida na kasar nan.
Hakan na nufin Arewa maso Yamma zai samu jihohi takwas, Arewa maso Gabas jihohi bakwai, Arewa ta Tsakiya jihohi bakwai, Kudu maso Yamma jihohi bakwai, Kudu maso Kudu jihohi bakwai da Kudu maso Gabas jihohi shida.
Za a gabatar da rahoto gaban majalisa
Wannan shawarar za ta zama ɓangare na rahoton kwamitin haɗin gwiwa wanda za a gabatarwa majalisar dattawa da majalisar wakilai a makon farko na watan Nuwamba.
Wani babban jami’i ya bayyana cewa dukkan ‘yan majalisun biyu sun amince da wannan mataki domin adalci da daidaito.

Source: Twitter
‘Yan majalisar sun kuma amince da kafa karamin kwamiti da zai gano inda za a fitar sababbin jihohin guda shida.
Babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Mohammed Tahir Monguno, ne ke jagorantar kwamitin.
Wani mamba daga Arewa maso Yamma ya tabbatar da cewa za su duba dukkan bukatun kirkiro jihohi 55 da aka tura wa majalisar don fitar da wuraren da sababbin jihohin za su fito.
“Za mu duba dukkan bukatun kirkirar jihohi 55 da kyau domin mu gano inda sababbin jihohi shida za su fito. Za mu yi adalci da gaskiya ga duk masu neman kirkirar jihohi."
- Wani mamba
Majalisa na son rage ikon shugaban kasa
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilai ta amince da.kudirin doka na biyu da ke neman tabbatar da 'yancin hukumar EFCC.
Daya daga cikin muhimman abubuwan da kudirin ya kunsa shi ne rage ikon shugaban kasa wajen cire shugaban EFCC.
Hakazalika sabon kudirin ya tanadi cewa dole sai majalisar dattawa da ta wakilai sun amince da kashi biyu bisa uku (2/3) kafin shugaban kasa ya iya cire shugaban EFCC daga mukaminsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


