Ana Wata ga Wata: Mai Wushirya Ya Fasa Auren 'Yar Guda, Ya Bayyana Dalili

Ana Wata ga Wata: Mai Wushirya Ya Fasa Auren 'Yar Guda, Ya Bayyana Dalili

  • Tun kafin magana ta yi nisa, shahararren dan TikTok, Ashiru Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya, ya kawo cikas a batun aurensa da Basira 'Yar Guda
  • Mai Wushirya ya bayyana cewa bai da wata masaniya kan kudin gudunmawa da ake karba da sunan aurensa da 'Yar Guda
  • Ya bayyana cewa tun da farko tsoro ne ya sanya ya amince da cewa zai auri 'Yar Guda wadda suke fitowa a cikin bidiyoyi tare da ita

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Shahararren dan TikTok, Ashiru Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya, ya kawo cikas a batun aurensa da Basira 'Yar Guda, wadda suke fitowa cikin bidiyoyi tare.

Mai Wushirya ya bayyana cewa ya fasa auren Basira 'Yar Guda, wadda kotu ta bada umarnin a daura musu aure.

Kara karanta wannan

Dakarun tsaron Najeriya sun harzuka, sun hallaka jagoran 'yan ta'adda a Filato

Mai Wushirya ya fasa auren 'Yar Guda
Ashiru Idris tare da Basira 'Yar Guda Hoto: Mai Wushirya
Source: Facebook

MeyasaMai Wushirya ya fasa auren 'Yar Guda?

Shahararren dan TikTok din ya bayyana hakan a cikin wani bidiyo da ya fitar wanda aka sanya a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ko lauyoyina ba da yawunsu na amsa zan yi aure ba don sun san bana so. Saboda ni gaskiya na ji tsoro ne kan lamarin."
"Su kuma 'yan uwana abin da suke ta wannan, idan ma aure zan yi, su meye rayuwarsu. Kaf gidanmu ni ne karami ya za a yi a ce za a yi min auren hukuma ko wani abu, har abokaina su fara min dariya ko a ga an yi min auren dole na zo na firgice."

- Mai Wushirya

Ya bayyana cewa ita kanta Basira 'Yar Guda ba ta son auren, domin ta fi son a je gaban iyayenta a auro ta kamar yadda ake yi wa kowace 'ya mace.

Ba ruwan Mai Wushirya da kudin gudunmawa

Kara karanta wannan

Wa ya kashe ta? Mahaifin ƴar jarida da ta mutu a Abuja ya aika sako ga ƴan sanda

Mai Wushirya ya bayyana cewa bada yawunsa ake hada kudaden gudunmawa kan auren ba, domin babu ruwansa a ciki.

Ya bayyana cewa bai sanar da cewa zai yi aure ba, don haka bai san da amsar kudin gudunmawa ba.

"Maganar kudin gudunmawa da ake tarawa wasu, ba wani sisi da ya zo wurina. Don haka duk wanda ya san ya tura kudi ko ta hannun waye, ni dai ba da yawuna ba."
"Kuma wadanda suka san sun karbi kudi, ni na sadaukar da kudin ga marayu ko kuma a kai gidajen gyaran hali a raba musu a saya musu wani abin."
"Idan ma aure ne wannan zan yi ko za ta yi, kuna da 'yancin na fito na gaya muku, idan ma akwai wanda zai taimake ta ya taimake ta, saboda tana bukatar taimako."

- Mai Wushirya

Mai Wushirya ya fasa aurensa da Basira 'Yar Guda
Basira 'Yar Guda tare da Ashiru Idris Mai Wushirya Hoto: Mai Wushirya
Source: Facebook

Mai Wushirya ya yi godiya

Hakazalika, Mai Wushirya ya godewa shugaban hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa, kan nasihohin da ya yi masa.

Ya kuma godewa alkaliyar da ta jagoranci shari'arsa saboda yadda ta tarbe shi cikin raha lokacin da ya je ofis din ta.

Kara karanta wannan

'Dan Najeriya ya yi amfani da kayan aikin mace, ya burma kansa a matsala a Ingila

'Yar Guda ta fadi sharadin auren Mai Wushirya

A wani labarin kuma, kun ji cewa Basira 'Yar Guda ta sanar da shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa, sharadin aurenta da Mai Wushirya.

'Yar Guda ta kafa sharadin cewa ba za ta zauna a gidan haya ko tare da 'yan uwan Mai Wushirya ba.

Sharadin na ta na zuwa ne bayan Sheikh Daurawa ya bayyana cewa shirye-shirye sun kankama kan aurar da matasan guda biyu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng