Sowore: An Firgita Masu Zanga Zanga, an Kama Mutanen Nnamdi Kanu a Abuja

Sowore: An Firgita Masu Zanga Zanga, an Kama Mutanen Nnamdi Kanu a Abuja

  • A yau Litinin ne 'yan sanda da sauran jami'an tsaro suka fatattaki masu zanga zangar neman a saki shugaban IPOB a Abuja
  • ’Yan sanda sun kama ɗan’uwan Nnamdi Kanu da lauyansa, Aloy Ejimakor, yayin da suke kokarin tarwatsa masu zanga-zangar
  • Omoyele Sowore ya zargi jami’an tsaro da yin amfani da karfi da kuma bugun masu zanga-zangar ba tare da wata hujja ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wasu jami’an ’yan sanda da aka tura domin dakile zanga-zangar neman sakin Nnamdi Kanu sun kama mutane.

An kama ɗan’uwan shugaban ƙungiyar IPOB da aka haramta, Nnamdi Kanu, tare da lauyansa Aloy Ejimakor, kamar yadda jagoran zanga-zangar, Omoyele Sowore, ya bayyana.

Sowore lokacin da ya ke gudu
Sowore na gudu bayan 'yan sanda sun tarwatsa masu zanga zanga. Hoto: Hassan Muhammad
Source: Facebook

Sowore ya wallafa a shafinsa na X cewa ’yan sanda sun kuma kama wasu mutane marasa laifi da ke wajen yayin da suke tarwatsa masu zanga-zangar da ke neman a saki Kanu.

Kara karanta wannan

Sakin Nnamdi Kanu: Sowore, 'yan zanga sun ruga da gudu bayan fara harbi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kanu dai na hannun hukuma tun bayan sake kama shi a watan Yuni 2021, bayan an tuhume shi da aikata laifuffukan da suka shafi tsaro da cin amanar kasa.

Yadda aka fara zanga-zangar Kanu

Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun toshe duk hanyoyin da ke kaiwa Unity Fountain – inda aka tsara fara zanga-zangar – tare da hana direbobi da masu tafiya ƙasa wucewa.

An ga motocin sojoji da ’yan sanda masu dauke da makamai suna sintiri a yankin, wanda hakan ya sa Unity Fountain da sauransu suka zama wuraren da babu damar shiga.

Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu da ake zanga zanga domin neman a sake shi. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Twitter

Rundunar haɗin gwiwa ta sojoji da ’yan sanda ta harba hayaki mai sa hawaye a kusa da ofishin ƙungiyar NUJ a unguwar Utako, inda mutane da ke wajen suka tarwatse.

Yele Sowore ya ce an farmake su

Da yake magana a tashar Channels Television a ranar Litinin, Sowore ya bayyana cewa masu shirya zanga-zangar sun sanar da ’yan sanda a gaba kafin fara gangamin.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu, an kama hatsabiban yan bindiga da suka hallaka Sarki Mai Martaba

Ya ce duk da wannan, an kama wasu daga cikin masu zanga-zangar tare da wasu jama’a da ke wucewa a wurin.

“An kai mana hari ba tare da wata rigima ba. Mun fara zanga-zangar cikin natsuwa a gaban Transcorp Hotel, amma nan da nan motocin ’yan sanda da sojoji suka cika wajen,”

- Inji Sowore

An kama dan uwa da lauyan Kanu

Sowore ya ce sun gaya wa 'yan sanda cewa su ba maƙiyansu ba ne, kuma wannan zanga-zanga ba ta shafe su ba.

Daily Trust ta wallafa cewa ya kara da cewa daga baya sai suka fara harba hayaki mai sa hawaye da harsasai:

"Duk da haka, ba mu ji an samu wanda harsashi ya same shi ba.”

A halin yanzu, an ruwaito cewa dan uwan Nnamdi Kanu da lauyansa Ejimakor, suna hannun ’yan sanda a FCT, yayin da ake kira ga hukumomi su sakesu nan da nan.

Gwamna Soludo ya magantu kan Kanu

Haka zalika, mun rahoto cewa Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya yi magana kan shugaban IPOB, Nnamdi Kanu mai neman ballewa daga Najeriya.

Kara karanta wannan

Zargin bata sunan hadimin Gwamna Abba: 'Yan sanda sun yi magana kan tsare dan jarida

Soludo ya bayyana cewa ba ya goyon bayan fita daga Najeriya domin a cewarsa, zamansu a Najeriya zai kawo cigaban Igbo.

Gwamnan ya bayyana cewa tsaro ya dawo a jiharsa sosai kuma a yanzu haka zaman gida da ake duk ranar Litinin ya ragu a Anambra.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng