Sarkin Musulmi Ya Magantu kan Neman 'Raba' Najeriya a gaban Gwamnoni a Legas

Sarkin Musulmi Ya Magantu kan Neman 'Raba' Najeriya a gaban Gwamnoni a Legas

  • Gwamnoni da dama sun bukaci a kafa doka da za ta bai wa sarakunan gargajiya matsayi a tsarin mulkin kasar nan
  • Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, da na Legas, Babajide Sanwo-Olu, sun ce rashin wannan matsayi babban gibi ne
  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya jaddada cewa babu wani da zai raba Najeriya, yana kira ga ’yan kasa su zauna lafiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas – Gwamnoni daga jihohi 10 a fadin kasar nan sun hadu da manyan sarakunan gargajiya a taron majalisar koli ta sarakunan Najeriya.

Gwamnonin sun bukaci a baiwa sarakunan matsayi a kundin tsarin mulki domin su taka rawar gani a tsarin mulki da zaman lafiya.

Sultan da wasu sarakuna
Sarkin Musulmi, Sarakuna da gwamnoni a Legas. Hoto: Babajide Sanwo Olu
Source: Facebook

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya wallafa abubuwan da aka tattauna a taron a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya hango mafita kan 'yan bindiga a sulhun Hamas da Isra'ila

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron ya samu halartar gwamnan Imo, Sanata Hope Uzodinma, da takwaransa na Legas, Babajide Sanwo-Olu da sauransu.

Maganar sa sarakuna a tsarin mulki

Gwamnan Imo, Hope Uzodinma, wanda ya bude taron a madadin Bola Tinubu, ya ce rashin ayyana matsayi ga sarakuna a kundin tsarin mulki babban gibi ne da ake bukatar cikawa.

Ya ce sarakunan gargajiya na taka muhimmiyar rawa wajen daidaita al’umma, sasanta rikice-rikice da kuma kare al’adun gargajiya, yana mai cewa:

“Srakuna su ne igiyar hadin kai da ke rike Najeriya wuri guda.”

Uzodinma ya yi kira ga majalisar dokoki ta kasa da sauran hukumomin gwamnati da su tallafa wa shirin ba sarakunan wannan matsayi.

Ya kara da cewa hakan ba gata ba ce, illa dai amincewa da rawar da suke takawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Gwamnan ya kuma ja hankalin sarakuna da su guji shiga harkar siyasa kai tsaye, yana cewa hakan na iya rage darajarsu a idon jama’a.

Kara karanta wannan

Edun: Rashin lafiya ya kama ministan Tinubu, ya gaza wakiltar Najeriya a Amurka

“Kada ku bari a jawo ku cikin siyasa. Yin taka tsan tsan ba rauni ba ne, alama ce ta hikima,”

- Inji shi.

Sanwo-Olu ya yaba wa Sarakunan gargajiya

A nasa jawabin, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce lokaci ya yi da za a fayyace rawar da sarakuna za su taka a tsarin mulki domin a yi amfani da tasirinsu wajen inganta shugabanci.

Ya bayyana cewa bayan samun ‘yancin kai, sarakuna kamar marigayi Oba Adesoji Aderemi sun taka rawar gani a siyasar kasa, amma mulkin soja ya rage muhimmancinsu a tafiyar mulki.

Sarakuna yayin taron a Legas
Sarakuna da wasu gwamnoni a jihar Legas. Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Source: Facebook

Martanin Sarkin Musulmi ga masu son raba kasa

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya jaddada cewa babu wani abu da zai iya raba Najeriya.

Daily Trust ta rahoto cewa ya yi magana yana kira ga ’yan kasa su kasance masu imani, hakuri, da addu’a wajen fuskantar kalubale.

Ya ce:

“Ba wanda zai iya karya hadin kanmu. Duk wahalar da muke fuskanta, za mu ci gaba da kasancewa kasa daya.”

Ya kuma yi kira ga shugabanni da su yi mulki cikin gaskiya da amana, domin su san cewa amanar Allah ce suke rike da ita.

Kara karanta wannan

An jero sunayen tsofaffin gwamnoni 2 da ka iya maye gurbin minista a gwamnatin Tinubu

A karshe, Ooni na Ife ya tunatar da gwamnonin cewa sarakuna ba abokan fafatawarsu ba ne, sai dai abokan hadin kai.

Namadi ya zama Sardaunan Zazzau

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo ya zama Sardaunan Zazzau.

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan na cikin manyan da suka halarci bikin nadin Sarautar a jihar Kaduna.

Jagoran 'yan adawa, Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran manyan kasa sun taya Namadi Sambo murnar sarautar da aka ba shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng