Hadimin Tinubu Ya Fadi Dalilin Jifar Najeriya da Zargin Ana Yi Wa Kiristocin Kisan Kare Dangi

Hadimin Tinubu Ya Fadi Dalilin Jifar Najeriya da Zargin Ana Yi Wa Kiristocin Kisan Kare Dangi

  • Ana ta tafka muhawara kan zargin da wasu ke yi na yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya
  • Hadimin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fito ya yi tsokaci kan zargin wanda wasu 'yan siyasar Amurka ke rurutawa
  • Daniel Bwala ya alakanta zargin kan matsayar da Najeriya ta dauka dangane da rikicin Isra'ila da Falasdinu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mai ba wa shugaban kasa Bola Tinubu, shawara kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya yi magana kan batun yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.

Daniel Bwala ya bayyana maganar cewa ana kisan kare dangi ga Kiristoci a Najeriya karya ce da wasu ke yadawa saboda matsayar kasar kan batun kafa kasashe biyu a rikicin da ke tsakanin Isra’ila da Falasɗinu.

Bwala ya yi watsi da batun yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya
Shugaban kasa Bola Tinubu da Daniel Bwala. Hoto: @OfficialABAT, @BwalaDaniel
Source: Twitter

Daniel Bwala ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a cikin wata hira da gidan talabijin na France24 a birnin Paris.

Kara karanta wannan

Majalisar Kolin Musulunci ta karyata batun kisan Kiristoci, ta caccaki CAN, Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya ta bukaci a kafa kasar Falasdinu

Hadimin na Tinubu ya bayyana cewa jawabin da Kashim Shettima, ya gabatar a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA), ne ya sa wasu daga cikin ‘yan kasashen Yamma ke yada wannan zargi na kisan Kiristoci.

A jawabin Shettima a taron UNGA a birnin New York, ya la’anci hare-haren da ake kai wa fararen hula tare da kiran a nemi mafita ta kafa kasashe biyu domin warware rikicin Isra’ila da Falasɗinu.

Me Bwala ya ce kan zargin kashe Kiristoci?

Daniel Bwala ya bayyana zargin kisan kare dangi ga Kiristoci a matsayin labarin bogi da kasashen Yamma suka kirkira saboda suna ganin tattalin arzikin Najeriya na samun ci gaba.

Ya ce wasu ‘yan siyasar Amurka da ke yada wannan magana suna dogaro da rahoton wasu kungiyoyi, wanda ya ce cike yake da kura-kurai.

"Mun yi watsi da batun cewa ana kisan kare dangi ga Kiristoci a Najeriya."

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa da aka ja kunnensu kan yin takara a 2027

“Mun amince cewa akwai matsalar tsaro a kasar, amma muna magance ta. Amma waɗanda ke kokarin bambance waɗanda matsalar tsaro ta shafa bisa addini, suna neman tada rikicin addini ne.”

- Daniel Bwala

Bwala ya ce gwamnatin Bola Tinubu tana samun nasarori a fannin tsaro, kuma maganganun da ke bambance mutanen da rikici ke shafa bisa addini suna nufin tada tarzoma tsakanin Musulmai da Kiristoci.

"Dalilin shi ne.. zan bada misali. A wajen taron UNGA, shugaban kasa ya samu wakilcin mataimakinsa, a cikin jawabinsa, Najeriya ta yi matsayar a samar da kasashe biyu kan rikicin Isra'ila da Falasdinu."
"Mun yi Allah da rashin imanin da ake yi a Gaza. Kwana guda bayan jawabin, wani ɗan barkwanci a Amurka mai suna Bill Maher ya fara wannan yaɗa labarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.”

- Daniel Bwala

Bwala ya kare Najeriya kan zargin kashe Kiristoci
Daniel Bwala a cikin wani ofis. Hoto: @BwalaDaniel
Source: Twitter

Lokacin da aka tambaye shi ko wannan zargi yana da alaƙa da matsayar Najeriya kan Gaza, sai Bwala ya ce "kwarai kuwa".

CAN ta aika sako ga gwamnati

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta koka kan hare-haren da ake kai wa Kiristoci.

Kara karanta wannan

Ana batun zargin kisan Kiristoci, yan bindiga sun yi ta'asa a masallacin Katsina

Kungiyar CAN ta nuna damuwar cewa al'ummar Kiristoci a sassa daban-daban musamman a yankin Arewa, na fuskantar hare-hare.

Ta bukaci gwamnatin tarayya da sauran hukumomin tsaro kan su tashi tsaye domin daukar matakin da ya dace.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng