PENGASSAN Ta Hukunta Rassanta 2 kan Rashin Hana Dangote Gas a Yajin Aiki
- Kungiyar PENGASSAN ta rusa shugabannin reshe na kamfanonin NGIC da NGML saboda gazawar tabbatar da yajin aikinta a kan matatar Dangote
- Gabanin rushe su, 'yan kungiyar kamfanonin biyu sun bukaci a janye zargin karbar cin hanci da hada baki da hukumar kamfanoni da ake yi masu
- Kungiyar ta ce shugabannin sun dauki matakai masu hatsari don cika umarnin yajin aikin kasa baki daya, amma duk da haka, ba a gani ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) ta rusa shugabannin rassan kamfanoni guda biyu.
Rassan da lamarin ya shafa sun hada da Nigeria Gas Infrastructure Company Ltd (NGIC) da NNPC Gas Marketing Limited (NGML).

Source: UGC
A labarin da ya kebanta ga jaridar The Cable, an gano cewa wannan mataki ya biyo bayan gazawar shugabannin wajen rufe iskar gas gaba daya ga matatar man Dangote.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yajin aikin da kungiyarta fara a ranar 28 ga Satumba, 2025, PENGASSAN ta nemi 'ya'yanta su hana iskar gas zuwa matatar Dangote.
'Yan kungiya sun fusata PENGASSAN
Rahotanni sun bayyana cewa an rusa shugabancin ne saboda zargin gaza cika umarnin kungiyar na rage samar da iskar gas ga matatar Dangote.
Hana matatar iskar gas na daga cikin manyan abubuwan da aka so a cimma a yayin yajin aikin nuna bacin rai da PENGASSAN ta tsunduma.
A cikin rahoton, 'yan NGIC/NGML sun roki shugabannin kasa na PENGASSAN da su sake duba hukuncin rushewar su da aka yi saboda ya yi tsauri.

Source: UGC
Haka kuma sun roki PENGASSAN ta janye zargin da ta ke yi mata na karbar kudi daga kamfanoni ko hada baki don hana rufe iskar gas.
Sun ce wannan zargi mai nauyi ne kuma yana iya bata suna da mutuncin shugabannin da ke aiki tukuru domin ci gabansu baki daya.
NGIC/NGML: Mun yi kokarin cika umarnin PENGASSAN
Kungiyar ta bayyana cewa, ko da yake ba a samu nasarar rufe gas gaba daya ba, sun kulle wasu daga cikin hanyoyin da ke kawo iskar gas zuwa Dangote daga layin OB3 ta Oben.
Sun bayyana cewa ba su taba cewa an rufe iskar gaba daya ba, sai dai suna fatan matakin zai kawo cikas ga yadda ake tafiyar da matatar.
Kungiyoyin biyu sun ce duk wani zargi na cin hanci ko cin amanar kungiyar ba shi da tushe, kuma matakan da shugabanninsu suka dauka sun hada da rufe wasu cibiyoyi.
Sun yi gargadin cewa cigaba da irin wadannan zarge-zarge na iya sa wasu daga cikin 'yan kungiyar da dama su yanke kauna daga daukar nauyin yajin aiki a nan gaba.
Gwamnati ta shiga tsakanin Dangote da PENGASSAN
A baya, kun ji cewa bayan kwanaki biyu na tattaunawa da shiga tsakani, gwamnatin tarayya ta samu nasarar kawo sulhu tsakanin kamfanin Dangote da PENGASSAN.
A sanarwar da Ministan Kwadago da Ayyukan Yi, Dr. Mohammed Maigari Dingyadi, ya fitar, an bayyana cewa an yi sulhu ne da hadin gwiwar bangarori da dama.
Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da aka amince da shi ne PENGASSAN ta janye yajin aikin da ta fara — wanda ake ganin zai iya kawo koma baya ga kasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


