Gwamna Ya Yi Aikin Ladan na Kiran Sallah a Masallaci, An Ga Bidiyon Abin da Ya Faru

Gwamna Ya Yi Aikin Ladan na Kiran Sallah a Masallaci, An Ga Bidiyon Abin da Ya Faru

  • Gwamma Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ba mutane da dama mamaki yayin da ya kira sallah a masallacin gidan gwammati
  • An ga Gwamna Bala, wanda shi ne shugaban gwamnonin PDP yana kiran sallah a wani faifan bidiyo da ke yawo a kafar sada zumunta
  • Mutane da dama sun yaba wa gwamnan bisa yadda yake kokarin kulawa da addininsa yayin da wasu ke ganin ba wani abin birgewa ba ne

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi (Kauran Bauchi) ya yi abin da ba kasafai ake samun gwamnoni ko manyan yan siyasa na yi ba.

Gwamna Bala ya kira sallah da kansa a masallacin gidan gwamnatinsa da ke cikin birnin Bauchi, lamarin da mutane da dama suka yaba tare da jinjina masa.

Kara karanta wannan

Triumph: An shawarci Abba game da kalaman mataimakinsa, Sagagi kan zargin taba annabi

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi.
Hoton gwamnan Bauchi, Bala Mohammed a gidan gwamnatinsa. Hoto: Sen. Bala Mohammed
Source: Twitter

Fitaccen mai amfani da kafar sada zumunta, Datti Assalafy ya wallafa bidiyon lokacin da gwamnan ke kiran sallah a shafinsa na Facebook ranar Asabar da ta wuce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Gwamna Bala ya kira sallah

A faifan bidiyon, an ga Gwamna Bala Mohammed ya dauki lasifika yana kiran sallah kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Duk ba a bayyana wace Sallah gwamnan ya yi ma kiran Sallah ba amma dai ana kyautata zaton ba zai wuce sallar Azahar ko La'asar ba, wadanda galibi ake yi a lokacin aiki.

Har ila yau faifan bidiyon ya nuna mutane sun shigo masallacin suna jiran Gwamna Bala ya gama kiran sallah, inda aka ga wasu na daukarsa a wayoyinsu.

Datti Assalafy ya yaba wa gwamnan bisa wannan hali mai kyau da ya nuna wanda wasu ke ganin alama ce da ke nuna yana sallah a jam'i.

A jikin bidiyon da ya wallafa, Datti ya rubuta cewa:

Kara karanta wannan

Abba ya jero bangarori 5 da gwamnatin Kano ta farfado da su a cikin shekaru 2

"Masha Allah, yadda mai girma gwamnan jiharmu na Bauchi, Kauran Daular Usmaniyya, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir ya kira Sallah a cikin Masallacin fadar gwamnatin jihar Bauchi.
"Abin ya burgeni gaskiya, muna matukar kaunar gwamnan jiharmu na Bauchi, muna kuma alfahari da shi. Allah Ya kara albarka a rayuwarsa da ta mu."

Mutane sun bayyana ra'ayoyinsu

Sai dai mutane sun mayar da martani mabanbanta, wasu sun yabi gwamnan tare da masa fatan alheri yayin da wasu ke ganin ba wani abin birgewa ba ne.

Tijjani Murtala ya ce:

"Masha Allah, gaskiya abun akwai ban sha'awa."

Abubakar Jiddah ya ce:

"Ni ma yana matukar burgeni saboda baya wasa da ibadah, jam'in sallah ba ya wuce shi, ko lokacin da yake Ministan Abuja mun je gidansa shan ruwa da azumi, da shi muka yi Magrib da Isha'i a jam'i. Ga shi da saukin kai, karamci da kyauta."

Kwamared Abubakar Yakubu ya ce:

"Babu wani abin birgewa a wannan, wallahi ya biya mutane hakin su shi ne abin birgewa."

Gwamna Bala ya kori Kwamishinar Mata

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed ya sallami Kwamishinar Harkokin Mata da Kananan Yara ta jihar Bauchi, Hajiya Zainab Baban-Takko.

Kara karanta wannan

An kwantar da gwamna a asibiti daga tafiya wani aiki a kasashen waje? Gaskiya ta fito

Gwamnan ya dauki wannan matakin ne a wani bangare na gyare-gyaren da ya yi a Majalisar Zartarwa ta Jihar Bauchi.

Sanata Bala Mohammed ya gode mata bisa gudummawar da ta bayar ga jihar, inda ya yi mata fatan nasara a duk abin da ta sanya a gaba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262