Gwamna Dauda Ya Yi Alhinin Rasuwar Tsohon Jakadan Najeriya da Ya Rasu Yana da Shekara 82

Gwamna Dauda Ya Yi Alhinin Rasuwar Tsohon Jakadan Najeriya da Ya Rasu Yana da Shekara 82

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi ta'aziyyar rasuwar tsohon Jakadan Najeriya a kasar Tunisia, Ambassada Muhammad Jabbi Maradun
  • Dauda Lawal ya bayyana marigayin a matsayin dattijon kasa wanda ya taka muhimmiyar rawar gani wajen fafutukar kafa jihar Zamfara
  • Marigayin ya yi bankwana da duniya ne a birnin tarayya Abuja bayan ya dauki lokaci yana jinyar rashin lafiya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi alhini mai zurfi kan rasuwar tsohon Jakadan Najeriya a kasar Tunisia, Ambasada Muhammad Jabbi Maradun.

Ambassada Muhammad Jabbi Maradun ya rasu ne a Abuja a ranar Asabar bayan ya sha fama da doguwar jinya ta rashin lafiya.

Gwamna Dauda Lawal ya yi jimamin rasuwar Ambassada Muhammad Jabbi Maradun
Gwamna Dauda Lawal tare da marigayi Ambassada Muhammad Jabbi Maradun. Hoto: Sulaiman Bala Idris
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Mai Mala Buni ya gwangwaje dan tsohon gwamna da mukami a gwamnatinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Dauda ya yi ta'aziyyar Muhammad Jabbi

Gwamna Dauda ya bayyana marigayin a matsayin dattijo nagari mai kishin kasa, wanda ya taka rawar gani wajen kafa jihar Zamfara.

“Cike da bakin ciki muke jimami kan rasuwar Ambassada Muhammad Jabbi Maradun, dattijon kasa nagari kuma ɗan asalin jiharmu ta jihar Zamfara."
"An haifi marigayi Ambasada Jabbi a ranar 12 ga Nuwamba, 1943 a karamar hukumar Maradun. Ya kasance Jakadan Najeriya a Tunisia daga shekarar 1999 zuwa 2003."

- Gwamna Dauda Lawal

Marigayin ya taka rawa wajen kafa Zamfara

Marigayin ya taka muhimmin matsayi a fafutukar samar da jihar Zamfara, kuma bayan kirkirarta, ya rike mukamin kwamishinan kasuwanci, masana’antu da yawon buɗe ido a lokacin mulkin soja na Kanal Jibril Bala Yakubu.

Haka kuma, marigayin ya kasance gogaggen ɗan siyasa, inda ya taɓa yin mu’amala da jam’iyyun PDP, GNPP, NPN da kuma NRC a lokuta daban-daban.

Sanarwar ta kara da cewa aikin gwamnati na karshe da ya yi shi ne a matsayin kwamishina a hukumar RMAFC daga shekarar 2005 zuwa 2015, inda ya yi aikin cike da kwarewa da gaskiya.

Kara karanta wannan

Duniya kenan: Tsohon kwamishina a gwamnatin APC ya riga mu gidan gaskiya

Dauda Lawal ya yi alhinin rasuwar Ambassada Muhammad Jabbi Maradun
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal. Hoto: Dauda Lawal
Source: Twitter

Gwamna Dauda ya yi addu'a

“Mukamin gwamnati na karshe da ya rike shi ne kwamishina a hukumar RMAFC, matsayin da ya rike cikin kwarewa tun daga shekarar 2005 zuwq 2015."
"A madadin gwamnati da al’ummar jihar Zamfara, muna mika ta’aziyyarmu ga iyalansa, masarautar Maradun da dukkan mutanen karamar hukumar Maradun bisa wannan babban rashi."
"Allah Ya gafarta masa, Ya yi masa rahama, Ya kuma sanya Aljanna Firdausi ta zama makwancinsa na karshe."

- Gwamna Dauda Lawal

Gwamna Dauda ya ba gwamnonin Arewa shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi kira da babbar murya ga gwamnoni 19 na jihohin yankin Arewacin Najeriya.

Gwamna Dauda ya bukaci gwamnonin da su zama tsintsiya madaurinki daya ta hanyar hadewa waje guda su rika magana da murya daya kan harkokin tsaro da tattalin arziki.

Dauda Lawal wanda ya yi wannan kiran a wajen wani taron da aka yi kan zuba jari da farfado da masana'antun Arewa, ya bukaci gwamnonin da su fifita hadin kai fiye da siyasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng