Nigeria @65: Jonathan Ya Aika da Muhimmin Sako ga 'Yan Najeriya
- Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya aika da sako don bikin murna cikar Najeriya shekara 65 da samun 'yancin kai
- Jonathan ya karfafa gwiwar 'yan Najeriya kan kada su yanke tsammanin cewa kasar nan za ta kai inda ake son ganin ta kai
- Tsohon shugaban kasan ya aminta da cewa Najeriya na fuskantar tarin matsaloli wadanda za su iya hana ta samun ci gaban da ya dace
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su karaya duk da ƙalubalen da ake ciki a halin yanzu.
Goodluck Jonathan ya bukaci 'yan Najeriya su ci gaba da fatan ganin kasar nan ta kai inda ake so.

Me Jonathan ya gayawa 'yan Najeriya?
Jaridar The Punch ta ce Jonathan ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na fatan alheri ga ‘yan Najeriya a lokacin bikin cika shekara 65 da samun ‘yancin kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalaman tsohon shugaban kasan sun fito ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Mista Okechukwu Eze, ya fitar a birnin Abuja ranar Laraba, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da labarin.
Goodluck Jonathan ya ce bikin samun 'yancin kan ya ba Najeriya damar tunani kan tafiyar da ta yi wajen gina kasa, ciki har da kalubalen da aka fuskanta da kuma manyan damarmakin da har yanzu ake da su.
"Gaskiya ne muna fuskantar kalubalen da kan iya gwada karfin fatanmu, rashin tsaro, matsin tattalin arziki, da kuma hukumomin da sau da dama suke kasa cika alkawuran inganta jin daɗi, zaman lafiya da tsaro."
"Amma a matsayinmu na ‘yan kasa, ba za mu yanke tsammani ba. Ya kamata mu ci gaba da fata da amanna kan manyan damarmakin da kasar nan take da su da irin juriyar jama’arta."
"Najeriya kasa ce da Allah Ya albarkace ta, mai yalwar kasa, albarkatun kasa marasa iyaka, kuma a sama da komai, tana da mutane masu basira da fikira."

Kara karanta wannan
Gwamna Fintiri ya yi afuwa ga masu laifi don murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun 'yanci
"Dumbin al’adunmu, iliminmu da hikimar mu sun ci gaba da bambanta ‘yan Najeriya a kowane bangaren rayuwa a gida da waje."
- Goodluck Jonathan

Source: Twitter
Wace shawara Jonathan ya ba 'yan Najeriya?
Goodluck Jonathan ya shawarci ‘yan Najeriya da su rika sanya kishin kasa wajen gudanar da ayyukansu.
"Mu ci gaba da yin amanna tare da sanin cewa kasar mu za ta kai inda ake so idan har muka ci gaba da jajircewa da hada kawunanmu."
“Allah Ya ci gaba da ɗaukaka kasarmu."
- Goodluck Jonathan
PDP ta yi bayanai kan matsayin Jonathan
A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar jam'iyyar adawa a Najeriya watau PDP, ta yi magana kan zaman Goodluck Jonathan mamba a cikinta.
Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa har yanzu tsohon shugaban kasan na Najeriya, cikakken mamba ne domin bai fita daga cikinta ba.
Mai magana da yawun PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya bayyana cewa a saninsu har yanzu Jonathan yana cikin jam'iyyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
