'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari, an Rasa Rayukan Jami'an Tsaro a Kwara

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari, an Rasa Rayukan Jami'an Tsaro a Kwara

  • An shiga jimami a jihar Kwara bayan 'yan bindiga dauke da makamai sun kai wani kazamin hari kan bayin Allah
  • 'Yan bindigan sun kai harin ne a wani gari da ke karamar hukumar Ifelodun inda suka hallaka jami'an tsaro
  • Majiyoyi sun bayyana cewa an rasa rayukan 'yan sa-kai da mafarauta sama 10 a yayin harin da 'yan bindigan suka kai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kwara - 'Yan bindiga sun hallaka akalla ‘yan sa-kai da mafarauta 15 a jihar Kwara.

'Yan bindigan sun kashe mutanen ne da safiyar ranar Lahadi lokacin da suka kai hari a garin Oke-Ode da ke karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara.

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro a Kwara
Jami'an rundunar 'yan sanda a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Bidiyon da jaridar The Punch ya samu ya nuna gawarwakin ‘yan sa-kan da aka kashe kwance a kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun yi barna a Kwara

Kara karanta wannan

Abin ya yi muni: An bayyana sunayen malami da mutum 4 da suka 'mutu' lokaci Guda a masallaci

Rahotanni sun ce an kuma sace mutane masu yawa da ba a tantance adadinsu ba a yayin harin, wanda ya jefa al’ummar garin cikin alhini.

Wani mamba na kungiyar ‘yan sa-kai ta garin, wanda aka bayyana da sunan Ajetunmobi, ya bayyana cewa gwamnati na ɓoye gaskiya ta hanyar cewa an fatattaki maharan.

"Tun ranar Asabar da daddare muna jin labarin cewa ‘yan bindiga suna kewaye da garin, mun kuma aika sakonni ga jami’an tsaro kan su yi shiri."
"Amma abin mamaki, da safe sai maharan suka suka fara hari daga inda ‘yan sa-kai ke gadin gari."

- Ajetunmobi

Ya ce, cikin wadanda aka kashe akwai mutanen garin da suka hada da Oji, Saheed Metubi, Baale Ógba Ayo, da sauransu.

Hakazalika ya kara da cewa an kai gawarwakin zuwa ofishin ‘yan sanda, yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa babban asibitin Share.

An zargi gwamnati da sakaci kan harin

Mamban na ‘yan sa-kai ya zargi gwamnati da gazawa wajen kare jama’a, yana mai cewa an dade da bayyana bayanan sirri kan yiwuwar kawo harin, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar da labarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka dan sanda, an yi awon gaba da jami'an tsaro

“Gwamnati ta gaza wajen babban aikinta. Tuni ake ta yada bayanai cewa za a kai hari Oke-Ode. To me ya sa aka janye sojoji?"

- Ajetunmobi

'Yan bindiga sun kashe 'yan sa-kai a Kwara
Taswirar jihar Kwara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mai 'yan sanda suka ce kan lamarin?

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Mai magana da yawun 'yan sandan ya bayana cewa za a fitar da sanarwa da zarar an samu cikakkun bayanai.

“Mun samu labarin harin. Ina jiran cikakkun rahotanni daga sassa daban-daban. Da zarar na samu, za mu sanar da ku.

- SP Adetoun Ejire-Adeyemi.

Jami'an tsaro sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar Danja da ke jihar Katsina.

'Yan bindigan sun yi yunkurin yin garkuwa da mutane yayin harin da suka kai a garin Dabai da daddare.

Jami'an tsaro sun samu nasarar hallaka daya daga cikinsu tare da cafke wani, sannan suka kubutar da mutanen da aka sace.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng