Kwana Ya Kare: Hadimin Gwamna Bago Ya Yi Bankwana da Duniya

Kwana Ya Kare: Hadimin Gwamna Bago Ya Yi Bankwana da Duniya

  • An yi rashi a jihar Neja bayan rasuwar hadimin Gwamna Mohammed Umaru Bago a ranar Asabar, 27 ga watan Satumban 2025
  • Marigayin wanda yake rike da mukamin sarauta, ya rasu ne bayan ya yi fama da wata 'yar gajeruwar rashin lafiya
  • Gwamna Bago ya aika sakon ta'aziyyarsa kan rasuwar marigayin wanda ya bayyana a matsayin mutum mai son ci gaban al'ummarsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Galadiman Raban Nupe, kuma mai ba Gwamna Mohammed Umar Bago shawara kan harkokin masarautu, Alhaji Gimba Abubakar, ya rasu.

Marigayin ya rasu ne a safiyar ranar Asabar, 27 ga watan Satumban 2025 bayan gajeruwar rashin lafiya.

Hadimin Gwamna Bago ya rasu
Gwamna Mohammed Umaru Bago da Galadiman Raban Nupe, marigayi Alh Gimba Abubakar Hoto: @Chiefpressngs
Source: Twitter

Hadimin Gwamna Bago ya rasu

Jaridar Leadership ta ce wata majiya daga iyalansa ta bayyana cewa marigayin yana cikin koshin lafiya a ranar Juma’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce ya ci gaba da harkokinsa ba tare da wata alama ta rashin lafiya da za ta iya nuna cewa ya kusa mutuwa ba.

Kara karanta wannan

An yi rashi: Shugaban karamar hukuma a Bauchi ya yi bankwana da duniya

"Da safe ya je asibiti da kansa, daga baya ne kawai aka sanar da mu cewa ya rasu."

- Wata majiya

Marigayin wanda ya fi shekara 50 a duniya, ya rasu ya bar mata uku da ‘ya’ya.

Gwamna Bago ya yi ta'aziyya

Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bayyana matukar bakin cikinsa bisa rasuwar Galadiman Raban Nupe.

Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai tsari da sadaukarwa wanda ya tsaya tsayin daka wajen gaskiya da adalci.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Bologi Ibrahim, ya fitar a shafinsa na X.

Gwamna Bago ya yi ta’aziyya ga Etsu Nupe kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Neja, Alhaji Yahaya Abubakar, da kuma masarautar Bida, bisa wannan babban rashi.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa kura-kuransa ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdausi, tare da rokon iyalansa su ci gaba da yi masa addu’ar neman rahamar Allah.

Gwamna Bago ya yi ta'aziyyar hadiminsa
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Ya kuma shawarci iyalan marigayin da su tabbatar da cewa an ci gaba da kiyaye kyawawan dabi’u da ayyukan alherin da yake yi.

Kara karanta wannan

Kazamin rikicin manoma ya firgita Darazo, ya hana zuwa gona a Bauchi

Gwamna Bago ya kara bayyana cewa marigayin yana daga cikin ‘ya’yan masarautar Nupe masu jajircewa wajen ci gaban yankinsu da kuma tallafawa al’umma baki ɗaya.

"Gwamna Bago ya kuma mika sakon ta'aziyyarsa ga Etsu Nupe kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Neja, Alh. Yahaya Abubakar da masarautar Bida bisa rasuwar dansu wanda yake kan gaba wajen kawo ci gaba a masarautar Nupe."

- Bologi Ibrahim

Shugaban karamar hukuma ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa daya daga cikin shugabannin kananan hukumomi a jihar Bauchi, ya riga mu gidan gaskiya.

Hon. Yakubu Garba Tela wanda yake shugabantar karamar hukumar Dabam ya rasu ne a ranar Asabar, 27 ga watan Satumban 2025.

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya yi ta'aziyyar marigayin wanda ya bayyana a matsayin bawan Allah mai jajircewa a hidimar jama'a da wayar da kan al'umma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng