Rigima Sabuwa: Ana Yi wa Dangote Barazana kan Matatarsa bayan Korar Ma'aikata
- Kungiyar PENGASSAN ta yi barazanar kawo tsaiko a matatar Aliko Dangote bisa zargin korar ma’aikata da dama
- Dangote ya ce an sallami wasu ma'aikata ne saboda aikata ba daidai ba, ba wai saboda shiga kungiyar PENGASSAN ba
- Matatar Dangote ta kuma sanar da dakatar da sayar da man fetur a Naira daga ranar Lahadi, 28, Satumba, 2025
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - Kungiyar ma’aikatan kamfanonin man fetur ta Najeriya, wato PENGASSAN, ta yi barazanar shiga yajin aiki da maida matatar Dangote wurin bore bayan korar ma’aikatanta.
PENGASSAN ta yi zargin cewa fiye da ma’aikata 800 aka kora saboda shiga kungiyar a ranar Alhamis, 25, Satumba, 2025.

Source: Getty Images
Punch ta wallafa cewa Aliko Dangote ya ce abin da ya faru wani bangare ne na sake fasalin aiki domin kare matatarsa daga barazana samun cikas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin PENGASSAN kan korar ma’aikatan
Sakataren kungiyar, Lumumba Okugbawa, ya ce an kori ma’aikatan ne saboda bin umarnin gwamnati na shiga PENGASSAN.
Ya ce tun da shugabancin matatar ya gano cewa ma’aikatan sun kammala shiga kungiyar, sai aka aike musu da wasikar sallama.
Kungiyar ta zargi kamfanin da fifita ma’aikatan Indiya sama da na Najeriya, inda aka ce sama da 2,000 daga cikinsu sun ci gaba da aiki ba tare da matsala ba.
Martanin matatar Dangote ga PENGASSAN
Matatar Dangote ta fitar da sanarwa tana mai cewa an sallami wasu ma’aikatan ne saboda matsalolin da suka fuskanta a wuraren aiki.
Sanarwar ta bayyana cewa sake fasalin da ake yi wajibi ne domin tabbatar da tsaro da ingancin matatar
Wasikar da ta bazu a kafafen sada zumunta ta nuna cewa an sallami dukkan ma’aikata, amma kamfanin ya musanta hakan, yana mai cewa ‘yan kadan ne abin ya shafa.

Source: Getty Images
Za a yi wa Dangote zanga-zanga
Kungiyar PENGASSAN ta yi barazanar cewa za ta iya daukar matakin bore ko kuma ta gudanar da zanga-zanga a gaban matatar Dangote.
Sai dai kamfanin ya riga ya samu umarnin kotu da ke hana toshe wuraren da matatar ke gudanar da ayyukanta.
Kungiyar ta ce duk da hakan, za ta ci gaba da kare ‘yancin ma’aikatanta ta kowace hanya da ta dace.
Dakatar da sayar da fetur a Naira
A wani labari da ya dabaibaye harkar man fetur, matatar Dangote ta sanar da cewa daga ranar Lahadi, 28, Satumba, 2025, za ta daina sayar da man fetur da Naira.
Vanguard ta wallafa cewa sanarwar da aka tura wa masu sayan mai ta bukaci su nemi maida musu kuɗinsu idan sun riga sun kulla ciniki da Naira da matatar.
An nemi tallafin mai wajen Dangote
A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya yi jawabi na musamman kan tallafin man fetur da aka nema a wajensa.
Rahotanni sun bayyana cewa Dangote ya ce wasu 'yan kasuwa ne suka nemi ya saka musu tallafin Naira tiriliyan 1.5.
Dangote ya bayyana karara cewa ba zai lamunci hakan ba, domin an yaudari gwamnatin Najeriya tsawon lokaci game da tallafi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


