Jonathan Ya Fadi Tsohon Ministan da Ya Kamata 'Yan Siyasa Su Yi Koyi da Shi
- Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana halayen kirki da tsohon ministan noma, Audu Ogbeh, yake da su
- Goodluck Jonathan ya bayyana Audu Ogbeh a matsayin mutum mai yafiya wanda ba ya riko a zuciyarsa
- Tsohon shugaban kasan ya nuna cewa yana da hali irin na marigayin wanda ya taba shugabantar jam'iyyar PDP
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa bai rike kowa a zuciyarsa kan abubuwan da aka taba yi masa a baya
Goodluck Jonathan ya jaddada cewa yafiya da sulhu suna da matukar muhimmanci a siyasa, haɗin kan kasa da ci gaba.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce ya bayyana hakan ne a daren Laraba a Abuja yayin taron addu’ar tunawa da tsohon ministan noma, Cif Audu Ogbeh.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jonathan ya fadi halayen Audu Ogbeh
A cewar sanarwar da mai magana da yawunsa, Ikechukwu Eze, ya fitar, Jonathan ya bayyana marigayi Ogbeh a matsayin mutum mai sauƙin kai kuma mai yafiya, wanda ba ya riko a zuciya, tamkar yadda shi ma yake ɗaukar rayuwa.
"Cif Ogbeh mutum ne wanda ba ya neman ramuwar gayya. Ya yi imani cewa abin da ya wuce ya wuce."
"A wannan fannin, yana kama da ni. Idan ka cutar da ni yau, zan yafe maka. Ban yin kiyayya da kowa. Na yi imani abin da ya wuce ya wuce."
- Goodluck Jonathan
Jonathan ya bayyana cewa alakarsa da marigayi Ogbeh ta fara ne tun lokacin da yake mataimakin gwamna, yayin da marigayin yake shugaban jam’iyyar PDP.
“Ban san Cif Ogbeh ba sai da na zama mataimakin gwamna, lokacin yana shugaban PDP. A lokacin, ana kallon mataimakan gwamna kamar ‘tayar ajiya’, amma ya ɗauke ni a matsayin aboki na kusa."
"Duk lokacin da na je Abuja, sai na kai ziyara wajensa, kuma muna yin tattaunawa mai ma'ana. Mutum ne mai kirki da karamci sosai."
- Goodluck Jonathan.
Ya kara da cewa zumuncin da ke tsakaninsu ya ci gaba har bayan da ya zama shugaban kasa, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da labarin.
“Duk lokacin da yake so ya ganni, yana zuwa, kuma wani lokaci muna iya yin sa’a guda muna tattauna batutuwan kasa."
- Goodluck Jonathan

Source: Facebook
Wace shawara Jonathan ya ba 'yan siyasa?
Jonathan ya yi kira ga ‘yan siyasar Najeriya da su yi koyi da dabi’un Ogbeh na saukin kai, yafiya da iya haɗa kan jama’a daga sassa daban-daban.
Tsohon shugaban kasan ya jaddada cewa irin waɗannan kyawawan dabi’u ne ginshikin ci gaban ƙasa.
PDP ta magantu kan takarar Jonathan
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta bayyana matsayarta kan takarar Goodluck Jonathan a zaben 2027.
Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa Jonathan yana da 'yancin yin takarar shugaban kasa a babban zaben shekarar 2027.
Hakazalika, jam'iyyar ta ce dole Goodluck Jonathan ya bi dukkan matakan da dokar jam’iyya ta shimfida don neman takarar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


