Asiri Ya Tonu: Gwamnatin Katsina Ta Gano Ma'aikatan Bogi sama da 3,000

Asiri Ya Tonu: Gwamnatin Katsina Ta Gano Ma'aikatan Bogi sama da 3,000

  • Gwamnatin Katsina ta gano wasu ma'aikata 3,488 da ake karbar albashi alhali na bogi ne, sannan ba sa zuwa aiki a wasu kananan hukumomin jihar
  • Gwamnati ta bayyana cewa wani kwamitin da ta kafa ne ya gano ma’aikatan da ke karɓar albashi fiye da ɗaya sannan ba sa aiki yadda ya kamata
  • Gwamnan jihar, Dikko Umaru Radda ya ce an dauki matakin da ya dace a kan ma'aikatan domin ta haka ne za a ceto sauran ma'aikatan jihar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoGwamnatin Jihar Katsina ta kori ma’aikata 3,488 daga ƙananan hukumomi da hukumomin ilimi na gundumomi (LEA) bayan tantance bayanansu.

Rahoton kwamitin da gwamnati ta kafa ya yi aikin ya nuna cewa an tantance ma’aikata 50,172, inda 46,380 kacal suka cika sharuddan da su ka dace.

Kara karanta wannan

Fursunoni a Kano sun yi jarrabawar NECO, kusan mutum 70 sun yi zarra

An gano ma'aikatan bogi a Katsina
Hoton Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda Hoto: Dikko Umaru Radda
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa rahoton kwamitin ya ce sauran kuwa an gano su da takardun bogi, guraben aikin da kuma sun ƙi bayyana gaba ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano ma'aikatan bogi a Katsina

Jaridar PM ta wallafa cewa an gabatar da cikakken rahoton kwamitin a taron Majalisar Zartarwa ta Jihar Katsina a ranar Laraba, inda aka mika sakamakon binciken ga Gwamna Dikko Radda.

Rahoton ya gano wasu da suka shiga aiki kafin shekaru su kai, da wadanda aka ba hayar kujerun aiki, da kuma wasu da ke karɓar albashi fiye da ɗaya.

Sannan an kwato Naira miliyan 4.6 daga hannun waɗanda suka karɓi albashi ba tare da aiki ba ko kuma suna hutun aiki.

An kori ma'aikatan bogi a Katsina
Taswiar jihar Katsina, inda aka gano ma'aikatan bogi Hoto: Legit.ng
Source: Original

Shugaban kwamitin, Abdullahi A. Gagare, ya bayyana cewa wani Babban Sakataren Ilimi na Zango LEA ya hada baki da wasu domin saka ma’aikatan bogi guda 24 ana karbe albashin.

Gwamnan Katsina ya ce ana bukatar gyara

Kara karanta wannan

Katsina: Kananan hukumomi 2 sun zauna da ƴan ta'adda ɗauke da mugayen makamai

Gwamna Umaru Dikko Radda ya ce wasu sun gargade shi cewa wannan tantancewa na iya zubar masa da farin jini a siyasa, amma ya ƙi janyewa saboda bukatar gyara a jihar.

Ya ce:

“Wani lokaci sai ka fuskanci gaskiya, ko da zai baka cikas a siyasa. Wannan tsarin yana buƙatar gyara domin a samu ci gaba."

Gwamnan ya ce za a a aiwatar da abubuwan da takardar ta kunsa, tare da bayyana cewa adadin kuɗin da aka tanada a matakin ƙananan hukumomi ya kai Naira biliyan 5.7.

A cewarsa, ƙananan hukumomi kamar Kafur, Malumfashi da Daura suna fama da biyan albashi saboda yawan ma’aikatan da ba na gaskiya ba.

Katsina: An kama masu karkatar da kudin taki

A baya, mun ruwaito cewa Hukumar Ƙorafe-ƙorafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Katsina (KTPCACC) ta fara zurfafa bincike kan zargin badakala a rabon taki mai rahusa.

Binciken ya shafi batan kuɗi da suka kai Naira miliyan 188.6 a shirye-shiryen da suka haɗa da rabon taki da kuma wasu da ake zargi da aikata zamba a Ma’aikatar Kuɗi ta jihar.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida zai rage bashin Ganduje, za a biya karin N5bn ga 'yan fansho a Kano

Sanarwar KTPCACC ta bayyana cewa binciken farko ya gano cewa kansiloli da jami’an raya unguwanni (CDOs) sun karkatar da Naira miliyan 46.06 daga shirin rabon taki mai rahusa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng