An Yi Rashi: Shahararren Dan Kasuwa a Najeriya, Ya Yi Bankwana da Duniya
- An yi rashi na daya daga cikin manyan 'yan kasuwa a Najeriya, Olorogun Oscar Ibru, sakamakon rashin lafiya
- Shahararren dan kasuwan ya yi fice wajen ba da tallafi ga mabukata a nahiyar Afrika musamman yara
- Rasuwarsa na zuwa ne kasa da shekara 10 bayan rasuwar mahaifinsa, Michael Ibru, wanda ya yi bankwana da duniya a shekarar 2016
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Babban ɗan marigayi Michael Ibru, wanda ya kafa kungiyar Ibru, Olorogun Oscar Ibru, ya yi bankwana da duniya.
Marigayi Olorogun Oscar Ibru wanda yake shahararren dan kasuwa ya rasu ne yana da shekara 67 a duniya.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta rahoto cewa wani dan uwan marigayin ya tabbatar da rasuwarsa a ranar Laraba, 24 ga watan Satumban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oscar Ibru ya yi bankwana da duniya
Olorogun Oscar Ibru dan kasuwa mai biliyoyi, ya rasu ne sakamakon wata cuta da ba a bayyana ba,
Rasuwarsa ta zo ne kasa da shekara 10 bayan rasuwar mahaifinsa, Michael Ibru, a shekarar 2016.
Ana sa ran za a sanar da shirye-shiryen jana’izarsa nan gaba kaɗan.
Wanene Olorogun Oscar Ibru?
Leadership ta ce an haifi Oscar Ibru a shekarar 1958. Ya halarci makarantar kwalejin Igbobi, kafin daga bisani ya tafi Amurka domin ci gaba da karatu.
Ya samu digirinsa na farko a kwalejin Skidmore, sannan ya yi digirin digirgir a jami'ar Atlanta.
Bayan dawowarsa Najeriya a shekarar 1983, Oscar Ibru ya shiga aikin jaridar The Guardian.
Baya ga harkokin kasuwanci, Oscar Ibru ya kasance mashahurin mai bada agaji. A matsayinsa na shugaban gidauniyar Dream Child, wata kungiya mai zaman kanta, ya yi amfani da kiɗa wajen karfafa gwiwa da tallafa wa yara ’yan Afrika.
Tare da haɗin gwiwar kungiyoyi kamar bankin duniya da KPMG, gidauniyar ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta rayuwar dubban yara a nahiyar Afirika.
A shekarar 2017, jami'ar Igbinedion ta karrama shi da digirin girmamawa, saboda gudunmawar da ya bayar a rayuwarsa ga al’umma.
Haka kuma, Oscar Ibru ya samu sarautar Otunba Boyejo na masarautar Ijebu, mukami da ya nuna matsayinsa a harkokin kasuwanci da kuma al’adun gargajiya.

Source: Twitter
An yi ta'aziyyar marigayi 'dan kasuwan
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya yi ta'aziyyar marigayin a shafinsa na X.
"Da ni da Olorogun Oscar Ibru mun hadu kwanan nan a wajen bikin cikar shekara 10 a kan karaga na Ooni Oba Okunade Sijuwade Olubise IIa a Harbor Point da ke tsibirin Victoria, Legas, inda muka dan tattauna kafin mu rabu."
"Ba mu sani ba ashe bankwana ne ga daya daga cikin manyan masu taimako a Najeriya. Allah ya ji kanka dan uwa."
- Dele Momodu
Abokin Atiku Abubakar ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa daya daga cikin abokan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya rasu.
Atiku ya sanar da rasuwar Alhaji Muhammad Baba Suleiman Jada (MB Suleiman Jada), wanda ya bayyana a matsayin abokinsa tun na yarinta.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar MAUTECH da ke birnin Yola.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

