Halin da Dan Majalisar Plateau Yake Ciki bayan 'Yan Bindiga Sun Sace Shi

Halin da Dan Majalisar Plateau Yake Ciki bayan 'Yan Bindiga Sun Sace Shi

  • 'Dan majalisar dokokin jihar Plateau da 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi ya shaki iskar 'yanci a halin yanzu
  • Laven Denty Jacob wanda ya ke wakiltar Pankshin ta Kudu a ya kubuta daga hannun 'yan bindigan da suka sace shi daga gidansa
  • Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dokokin Plateau ya yi magana kan biyan kudin fansa kafin 'yan bindigan su sako Laven Denty Jacob

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Ɗan majalisar dokokin jihar Plateau mai wakiltar Pankshin ta Kudu, Laven Denty Jacob, ya kubuta daga hannun 'yan bindiga.

'Dan majalisar ya shaki iskar 'yanci ne bayan 'yan bindiga sun sace shi a gidansa da ke Anguwan Kagji a yankin Dongg, cikin karamar hukumar Jos ta Arewa, a daren ranar Litinin, 22 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa Gabdi ya ce gwamnoni ne matsalar kasar nan, ya ba talakawa shawara

Dan majalisar Plateau ya kubuta daga hannun 'yan bindiga
Hoton gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang Hoto: @CalebMutfwang
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar dokokin jihar Plateau, Hon. Kwarpo Sylvanus, ya tabbatar da sakin Laven Denty Jacob a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan majalisar Plateau ya shaki iskar 'yanci

Ya bayyana cewa an sake shi kuma tuni ya haɗu da iyalinsa cikin koshin lafiya.

"An sake shi cikin koshin lafiya, amma har yanzu ba mu tabbatar da ko an biya kuɗin fansa ko ba a biya ba. Abin da muka sani shi ne, an sake shi a daren jiya Talata."

- Hon. Kwarpo Sylvanus

Ya kara da cewa ɗan majalisar yana cikin koshin lafiya da kuzari.

Hon. Kwarpo Sylvanus ya yi kira ga mazauna yankin da su kasance masu sanya ido kan batun tsaro, tare da bayar da rahoto idan sun ga wani abin da bai dace ba a cikin yankunansu.

An yabawa jami'an tsaro

Ya yaba kan kokarin da jami’an tsaro suka yi da kuma haɗin kan da al’umma suka bada.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara, an yi awon gaba da mutane masu yawa

Hakazalika ya karfafa musu gwiwar ci gaba da kafa kungiyoyin sa-kai domin kare yankunansu duba da yadda matsalar rashin tsaro ta ki ci, ta ki cinyewa a wurare da dama.

“Mu ’yan majalisa za mu ci gaba da yin fafutukar samar da dokoki da za su larfafa tsarin tsaro a jihar."

- Hon. Kwarpo Sylvanus

An sace ɗan majalisar ne kwanaki 10 kacal bayan da aka yi garkuwa da wani mai yi wa kasa hidima (NYSC) da kuma wani ɗalibin jami’ar Jos a yankin.

Dan majalisar Plateau ya kubuta daga hannun 'yan bindiga
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga

'Yan bindiga sun sace basarake a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Plateau.

'Yan bindigan sun yi garkuwa da Hakimin Birbyang, Alhaji Zubairu Usman, tare da wasu mata guda biyu a harin da suka kai a karamar hukumar Kanam.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza kazamin fada da 'yan bindiga, an samu asarar rayuka

Tantiran 'yan bindigan sun shiga kauyen ne suna harbi kan mai uwa da wabi kafin daga bisani su yi garkuwa da Hakimin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng