Majalisar Tarayyar Najeriya Ta Dage Ranar Dawowa, Za a Kara Hutun Makonni 2

Majalisar Tarayyar Najeriya Ta Dage Ranar Dawowa, Za a Kara Hutun Makonni 2

  • Majalisar Tarayya ta dage dawowar zaman majalisa na gaba daga yau, Talata 23 ga watan Satumba, 2025 kamar yadda aka tsara a baya
  • Shugabannin majalisar sun tura sakonni ga sanatoci da 'yan majalisar wakilai tare da bada hakuri bisa wannan kara hutu da aka yi
  • Sai dai duk da dage zaman, majalisa ba ta bayyana dalilan da su ka jawo aka dage zaman ba zuwa watan Oktoba mai kamawa nan da kwanaki shida

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, AbujaMajalisar Tarayya ta Najeriya ta sanar da dage dawowar zaman majalisa da aka shirya a wannan watan da makonni biyu.

Kafin wannan sanarwar, an shirya cewa za a dawo zaman majalisa a ranar Talata, 23 ga Satumba, 2025, amma yanzu an mayar da ranar zuwa Talata, 7 ga Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

Zaman sulhu: Sheikh Gumi ya gargadi jami'an tsaro kan 'yan ta'adda

An dage ranar dawo wa hutun majalisar dattawa da na wakilai
Hoton zauren majalisar dattawa, da wasu 'yan majalisar wakilai Hoto: The Nigerian Senate/Abbas Tajuddeen
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa wannan na kunshe ne cikin wata takarda da Chinedu Akubueze, shugaban ma’aikatan shugaban majalisar dattijai, ya aikewa da sanatoci.

An dage zaman majalisar tarayya

The Nation ta ruwaito cewa a cikin takardar, Akubueze ya bayyana matukar nadama game da yadda wannan canji zai iya janyo cikas ga tsare-tsaren sanatocin.

Sanarwar ta bayyana cewa:

“Muna neman afuwa bisa wannan jinkiri. An dage dawowar zaman majalisa zuwa Talata, 7 ga Oktoba, 2025. Don haka, ana bukatar sanatoci su daidaita jadawalin aikinsu da sabon lokaci."

Takardar ta kuma bukaci sanatoci da su lura da wannan sauyi tare da yin duk gyare-gyaren da ya dace kafin ranar da aka sa za su dawo bakin aiki.

Ba a fadi dalilin dage zaman Majalisa ba

Haka zalika, Akawun Majalisar Wakilai, Yahaya Danzaria, ya aike da irin wannan sanarwa ga 'yan majalisar wakilai, inda ya tabbatar da dagewar zaman nasu.

Kara karanta wannan

Katsina: Kananan hukumomi 2 sun zauna da ƴan ta'adda ɗauke da mugayen makamai

A cikin wata takarda da aka rubuta a ranar 22 ga Satumba, 2025, Danzaria ya ce:

“Da matukar nadama muke sanar da cewa an dage zaman majalisa da aka shirya ranar 23 ga Satumba. Sabuwar rana ita ce Talata, 7 ga Oktoba, 2025.”
Za a dawo zaman majalisa a watan gobe
Hoton wasu daga cikin yan majalisar wakilai Hoto: House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Source: Facebook

Ya bukaci 'yan majalisa su lura da sabon jadawalin tare da yin sauye-sauyen da suka dace domin dacewa da sabon lokaci.

Sai dai ba a bayyana dalilin wannan jinkiri ba, lamarin da ya bar al’umma da masu lura da harkokin majalisa cikin zullumi.

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake sa ran majalisar za ta dawo da muhimman batutuwa da suka shafi kasafin kudi da sauran harkokin dokoki.

Majalisa ta karawa Gwamna karfi

A baya, mun wallafa cewa Majalisar Dokokin Adamawa a ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba, 2025, ta amince da wani muhimmin kudiri da ya yi gyara ga Dokar Nada da Sauke Sarakuna ta jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa majalisar ta amince da kudirin ne bayan karɓar rahoton daga kwamitin wucin gadin da aka kafa domin duba dokokin masarautu a tsanake.

Kara karanta wannan

Sakkwato: Shugabannin makarantun sakandare 6 sun tsunduma kansu a matsala

Mataimakin Kakakin Majalisar, Hon. Mohammed Buba Jijiwa, shi ne ya jagoranci wannan kwamitin, inda ya gabatar da cikakken rahoto a zaman da aka gudanar a ranar 17 ga watan Satumba, 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng