Wike Ya Sake Ballo Aiki, Ya Fadi Manyan Abubuwan da Ya Damu da Su
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan sukar da mutane ke yi masa
- Nyesom Wike ya bayyana cewa ko kadan bai taba damuwa da abin da mutane suke fadi a kansa ba
- Ministan ya bayyana cewa babban abin da ya fi maida hankali kan yin aikin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ba zai taɓa bari batanci ko sukar jama’a su yi tasiri a kansa ba.
Wike ya jaddada cewa damuwarsa ita ce yadda zai farantawa Allah da kuma yin aikinsa kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya umurce shi.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce Wike ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da aikin gina hanyoyin unguwar Mabushi, Abuja, a ranar Litinin, 22 ga watan Satumban 2025.
Nyesom Wike ya caccaki masu sukarsa
Wike ya yi kaca-kaca da masu sukarsa, yana zarginsu da kokarin amfani da batanci domin tilasta shi ya aikata abin da bai dace da ka’idarsa ba.
"To idan kuna so, ku tashi ku shirya kanku, kan wani abu da na sani ba daidai ba ne, idan kun ga dama ku yi kuka daga safe har dare, ku kira ni duk sunan da kuke so, ku saka sunana a intanet, ku faɗi duk abin da kuke so, babu matsala."
- Nyesom Wike
Wike ya jaddada cewa batanci wani abu ne da aka saba yakar 'yan siyasa da shi, amma bai isa ya sauya masa ra’ayi ba.
“Ni ba ni daga cikin waɗanda za ku yi tunanin batanci zai canja su. A matsayinka na ɗan siyasa, ya kamata ka sani cewa dole ne ka fuskanci irin waɗannan abubuwa, don me za ka damu?"
"Babu wani ɗan siyasa da ya daɗe a siyasa da zai yi tunanin mutane ba za su fadi wani abu a kansa ba."
- Nyesom Wike
Wane abu ne ya damu Wike?
Ya kara da cewa abin da kawai zai iya damunsa shi ne idan Shugaba Tinubu ya nuna rashin gamsuwa da aikinsa, rahoton Daily Post ya tabbatar da labarin.

Source: Facebook
“Ranar da na shiga siyasa, na san cewa daga yanzu mutane za su fadi duk abin da suke so, don haka ku faɗa. Abin da kawai zai dame ni shi ne idan wanda ya naɗa ni bai gamsu da aikina ba."
"Amma saboda kawai ba mu yi abin da kuke so ba, sai ku yi zaton batanci zai tilasta mu yi, ba za mu yi ba."
"Ban taɓa cewa ina son na kasance cikin mutanen da ake so ba. A’a, ban son wani ya so ni. Abin da nake so kawai shi ne Allah."
- Nyesom Wike
Wike ya aika sako ga Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Wike ya yabawa shugaban kasan ne kan matakin da ya dauka na janye dokar ta-bacin da ya sanya a jihar Rivers.
Ministan ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya sake nuna jajircewarsa wajen tabbatar da dorewar dimokuradiyya.
Asali: Legit.ng


